An Kafa Gwamnatin Rikon Kwarya A Kasar Burkina Faso.
Shugaban kasar Burkina Faso na rikon kwarya Paul-Henri Damiba ya kafa gwamnatin rikon kwara wacce ta kunshi har da ministan tsaron a gwamnatin Roch Kabore da aka yiwa juyin mulki.
Shafin yanar gizo na labarai ‘Afrika news’ ya bayyana cewa a ranar laraban da ta gabata ce aka rantsar da Damiba a matsayin shugaban kasa na gwamnatin rikon kwarya ta shekaru uku.
Sojojin kasar Burkina Faso sun kwace mulki ne a cikin watan Jenerun da ya gabata, inda suke korafi kan tabarbarewar harkokin tsaron kasar, da wannan manufar suka ga yakamata su shiga cikin lamarin don ceton kasar.
READ MORE : Daidaita Dangantaka Tsakanin Larabawa Da Isra’ila Barazana Ce Ga Falasdinawa.
Sabuwar gwamnatin da shugaban ya kafa a jiya dai ta kunshi ministoci 25 daga cikin har da tsohon ministan tsaro a gwamnatin da suka yiwa juyin mulki wato Janar Barthelemy Simpore.
A ranar Alhamis ce shugaban ya nada Albert Ouedraogo a matsayin shugaban gwamnati ko kuma firai ministan na gwamnatin rikon kwaryar.