An gargaɗi mazauna Delhi su zauna cikin shiri saboda mamakon ruwan sama
Ana ci gaba da zabga ruwan sama mai karfi a arewacin Indiya, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 20 tun daga ranar Asabar.
Mummunan yanayi – wanda ake sa ran zai ci gaba har zuwa ranar Juma’a – ya rushe bishiyoyi, da ambaliyar ruwa da kuma rufe manyan tituna a jihohi da dama.
A ranar Talata, Delhi ta kasance cikin shirin ko-ta-kwana don ambaliya yayin da ruwan kogin Yamuna ya kai wani mataki mai hatsari.
Tuni dai jami’ai suka mayar da dubban mutanen da ke zaune a kusa da gaɓar kogin zuwa wurare marasa hatsari.
Haka-zalika an gaya wa mazauna wasu yankunan da ke da rauni da su shirya domin a kwashe su zuwa tudun tsira idan bukatar hakan ya taso.
An katse zirga-zirgar ababen hawa a kan wata babbar gada da ta ratsa kan kogin, sannan an rufe makarantu a cikin kwanaki biyu sakamakon ruwan sama mai karfin gaske.
Babban Ministan Delhi Arvind Kejriwal ya ce kwanaki biyu masu zuwa za su iya kasancewa masu wuya ga birnin, amma ya kara da cewa gwamnatinsa a shirye take don tinkarar duk wani yanayi.