An dawo da gawar sojan haya dan Zambia da aka kashe a yakin Ukraine Gida.
A ranar Lahadi ne aka dawo da gawar sojar hayar nan dan Zambia da aka kashe a yakin Ukraine gida.
An kashe Lemekhani Nathan, ne a watan da ya wuce.
Kungiyar sojojin haya ta Wagner da ke Rasha ta ce ta dauki matashin ne haya daga daya daga cikin gidajen yarinta a inda ya ke zaman daurin rai da rai saboda ta’ammali ta miyagun kwayoyi.
Wagner ta ce da kanshi ya bukaci shiga cikin kungiyar.
Gwamnatin Zambia dai ta bukaci a yi mata cikakken bayani a kan mutuwar matashin dan kasarta.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ta rawaito mai magana da yawun iyalan mamacin na cewa an kai gawarsa zuwa dakin ajiye gawa don yin bincike inda daga bisani kuma za a sanar da ranar da za a binne shi.
Read More :
Sau biyar ina yunkurin sasantawa da Wike – Atiku.
Kayyade kudaden da za a cire a kullum zai fi shafar ‘yan siyasa ba talakawa ba – Sanusi II
Kwamitin Yaki Da ’Yan Daba Ya Rusa Ofishin Yakin Neman Zaben APC.
Imo: ‘Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Ofishin INEC.
Kofin Duniya 2022: Falasdinu ta doke Isra’ila a babban matakin kwallon kafa.