An bude taron hadaka na tsakanin Afrika da Turkiyya a wannan Juma’a a Santambul. Taron zai kuma samu halartar shugabanni da gwamnatin kasashen Afrika 16, baya ga ministocin harkokin waje 26 a wannan Asabar.
Turkiyya ta ce za ta taimaka wa nahiyar wajen yaki da annobar korona ta hanyar samar mata da alluran riga kafi miliyan 2,5.
Ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlüt Tchavoucholou, ya kuma jadadda shirin kasarsa na taimakawa harkokin tsaro da karfafa alaka da shinfida zaman lafiya a Afrika.