Amurka ta gargadi Mali game da amfani sojin hayar kamfanin Wagner na Rasha wajen yakar ayyukan ta’addanci da hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi da suka addabi kasar.
Sakataren harkokin wajen Amurkan Antony Blinken ya ce yarjejeniyar kasar ta yammacin Afrika da kamfanin ba komai za ta haifar face sake wargaza tsaron kasashen nahiyar.
Kalaman na Blinken da ke zuwa kwanaki 2 bayan Tarayyar Turai ta bi sahun Amurka wajen sanya takunkumai kan kamfanin na Wagner, ya ce abin takaici ne yadda kasar karkashin mulkin Soji ta yi watsi da bukatar kara mata yawan dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya don magance matsalar tsaron.
Sanarwar gargadin da sakataren amurka ya fitar, ta bayyana kamfanin na Wagner a matsayin wanda ya yi kaurin suna wajen take hakkin dan adam da kuma damalmala matsalolin tsaron da kasa ke fuskanta da zarar ya sanya kafa cikinta.
Sanarwar ta ruwaito Blinken na rokon gwamnatin rikon kwaryar ta Mali da ta yi amfani da miliyoyin kudin da za ta biya sojin hayar na Wagner kan dakarunta na cikin gida don karfafa musu gwiwa wajen yakar ta’addancin kasar.
A wani labarin na daban kuma shugabannin kasashen Afrika ta yamma sun kakaba wa jagororin juyin mulkin Guinea takunkumi, kana suka bukaci a gudanar da zabe nan da watanni 6 don maido da mulkin demokaradiyya cikin hanzari a kasar, bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin Alpha Conde a farkon wannan wata.
Ta yi kira ga kungiyar Tarayyar Afirka da ta Tarayyar Turai da su goyi bayan takunkuman da da ta kakaba wa gungun sojojin da suka yi juyin mulkin, wadanda suka kira kansu da kwamitin sansantawa da kawo ci gaba.
Kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO mai mambobi 15 ta riga ta dakatar da Guinea sakamakon juyin mulkin na ranar 5 ga watan Satumba da jagoran dakaru na musamman a kasar Kanar Mamady Doumbouya ya yi.
Wannan juyin mulki da sojoji suka yi a kasar Guinea ya janyo damuwa a tsakanin kasashen duniya ganin yadda demokaradiyya ke gamuwa da koma baya a yammacin Afirka, duba da yadda Mali ta gamu da juyin mulki har 2 tun a watan Agustan bara.
Sai dai a jawabinsa ga masu su ruwa da tsaki a siyasar kasar, jagoran juyin mulkin Guinea, Kanar Mamady Dombouya, ya jaddada cewa gazawar ilahirin ‘yan siyasan kasar ce ta tilasta masa kifar da gwamnatin farar hula.