Korarren dan takarar gwamna na PDP a jihar Kano, Sadiq Aminu Wali, ya bayyana niyarsa na zuwa kotun daukaka kara bayan babban kotun tarayya ta soke zabensa da aka yi a matsayin dan takarar gwamna a jihar.
Daily Trust ta rahoto cewa Babban Kotun Tarayya da ke Kano ta ayyana Mohammed Sani Abacha a matsayin halastaccen dan takarar gwamna na PDP a Kano.
A yayin yanke hukuncin, Mai shari’a A.M. Liman ya umurci hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta sauya sunan Wali da na Abacha.
Daga nan kotun ta amince da zaben fidda gwani na bangaren Shehu Sagagi da aka gudanar a Lugard House, wacce ta samar da Abacha a matsayin dan takarar gwamna a maimakon na bangaren Wali da aka gudanar a cibiyar matasa na Sani Abacha.
Martanin Aminu Wali Da ya ke magana da yan jarida a Kano, Wali ya yi kira ga magoya bayan PDP su kwantar da hankulansu, yana mai cewa lauyoyinsa na nazarin ‘hukuncin mai dauke da kuskure’ domin daukaka kara.
A cewarsa, lauyoyinsa tuni sun gano kura-kurai a hukuncin, wacce ta bashi kwarin gwiwa na kwato abin da ya kira ‘ikon da Kanawa’ a kotun daukaka kara.
Mun gano kura-kurai fiye da 20 a hukuncin koran Wali, Nasir Aliyu
A bangarensa, lauyan Wali, Nasir Adamu Aliyu (SAN) ya ce sun gano kura-kurai fiye da 20 don kare kansu a kotun daukaka kara, Daily Trust ta rahoto.
A cewar Aliyu, Wali ya yi nasara a kotun daukaka kara lokacin da Ja’afar Sani Bello ya shigar da kara yana kalubalantar zaben fidda gwani bayan an yi zabe bisa ka’ida kum jam’iyyar PDP ta kasa ta sa ido a kai.
Tunda farko, kun ji cewa Kotun tarayya a jihar Kano, a ranar Alhamis, ta tabbatar da Mohammed Sani Abacha, a matsayin halastaccen zababben dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano.
Mai sharia AM Liman, yayin hukuncin da ya yanke a ranar Alhamis ya soke zaben fidda gwani da ta samar da Sadik Aminu Wali.
Hakazalika, kotun da bawa hukumar zabe mai zaman kanta INEC umurnin ta sauya sunan Wali da na Mohammed Sani Abacha a cewar rahoton The Punch.