Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa (NiMET), ta gargadi wasu kananan hukumomi 14 daga cikin 44 na Jihar Kano, cewar za su iya fuskantar iftila’in ambaliyar ruwa a damina mai zuwa.
Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin ko’odinetan shiyyar Kano da Jigawa, Dokta Nuradeen Abdullahi, a yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan ambaliyar ruwa.
Kananan hukumomin da za su iya fuskantar barazanar sun hada da Rimin Gado, Tofa, Kabo, Madobi, Garum Malam, Bebeji, Rano, Dawakin Kudu, Warawa, Wudil, Sumaila, Ajingi, Kura da Dala
Sauran kananan hukumomin guda biyar su ne, Karaye, Takai, Bunkure, Dawakin Tofa, da Makoda, sai dai su ana hasashen ambaliyar ba lallai ta girmama kamar ta sauran ba.
Babban abin jan hankali a nan shi hanyoyin da za a bi domin magance barazanar aukuwar ambaliyar ruwa a daminar da ke tafe.
Dakta Abdullahi ya jaddada muhimmancin hada hannu da hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Kano (SEMA), domin tabbatar da cewa masu ruwa da tsaki sun shirya tsaf domin dakile barazanar.
“Mata da yara kanana sun fi zama masu rauni a lokacin damina,” in ji Dokta Abdullahi.
Amma ya bukaci mazauna yankunan da ka iya fuskantar ambaliyar ruwan, da su zauna cikin shiri da kuma bin matakan kariya.
Da ta ke bayani dangane da lamarin, kwamishiniyar jin-kai da kawar da talauci ta jihar, Hajiya Amina Abdullahi, ta tabbatar da kokarin gwamnatin jihar na hana aukuwar ambaliyar ruwan.
DUBA NAN: Jam’iyyar APC Tazo Ne Domin Talakawan Adamawa
Ta ce gwamnatin ta kafa wani kwamiti mai karfi, karkashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, wanda aka dora wa alhakin tsaftace magudanan ruwa a dukkanin kananan hukumomin jihar domin dakile hatsarin ambaliyar ruwa.