Kungiyar Kwadago A Najeriya Ta yi Kira Ga Alummar Kasar Da su shirya Shiga Zanga –Zanga
Rahotanni dake fitowa daga Nigeria sun nuna cewa Kungiyar kwadago ta NLC a Najeriya ta yi kira ga mata yan kasuwa da dalibai da sauran bangarori daban daban na kasa da su gyara damarar shiga gagarumar zanga-zangar kasa baki daya ta kalubalantar Karin kudin manfetur da dangoginsa da gwammati ke shirin yi, daga Naira 162 zuwa 304 kan kowacce lita
Shugaban kungiyar ta NLC reshin birnin Abuja kwamared Alhassan Yakubu ne ya bayyana hakan a wajen wani taron gangami da suka gudanar da kungiyoyin farar hula ,kana ya bayyana matsayin na rashin Adalci kuma ya sabawa muradun Alummar kasar.
Daga karshe ya kara da cewa Ma’aikata da sauran kungiyoyin farar hula a jahohi 36 a fadin kasar za su fara gudanar da gagarumar zanga-zanga a ranar 27 ga watan Janerun da muke ciki, inda za’a yi ta kasa baki daya a ranar 2 ga watan fabareru a birnin Tarayya Abuja.