Mutuwa ta sake fada wa kan dan majalisa kuma shugaban masu rinjaye a majalisa dokokin jihar Anambra, Nnamdi Okafor.
Okafor, wanda ke wakiltar Awka-South 1 a majalisar, Aallah yayi masa mutuwa ne a kasar Afirka ta Kudu a daren ranar Talata 23 ga watan Agusta a cewar rahotanni.
Ba a riga an tabbatar da sanadin rasuwar dan majalisar ba a har lokacin da aka kammala hada wannan rahoton.
Honarabul Nnamdi Okafor, Shugaban masu rinjaye na majalisar jihar Anambra ya riga mu gidan gaskiya.
Okafor ya rasu ne a daren ranar Talata a Afirka ta Kudu kamar yadda The Nation ta rahoto.
Dan Majalisar Anambra.
Okafor, wanda Allah yayi wa mutuwa dan majalisa wanda ya ke zangonsa na biyu, yana wakiltar mazabar Awka-South 1 a majalisar jihar.
Ya shiga majalisar jihar ne a shekarar 2015 a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA).
A halin yanzu babu cikakken bayani kan abin da ya yi sanadin rasuwarsa amma wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce ya yanke jiki ya fadi ne a otel din Sandton City, Johannesburg, Afrika ta Kudu, daga bisani aka tabbatar ya mutu, The Punch ta rahoto.
Kungiyar yan Najeriya mazauna kasar Afirka ta Kudu ta tabbatar da rasuwar dan majalisar, inda ta ce dan majalisar ya tafi Afirka ta Kudu don wani horaswa ne amma ya rasu awanni kafin dawowa Najeriya.
A wani rahoton, Mbazulike Iloka, dakataccen shugaban kwamitin mika mulki na karamar hukumar Nnewi ta Arewa a Jihar Anambra, ya shiga hannun yan sanda a jihar kan zarginsa da hannu kan mutuwar matarsa.
Kakakin yan sandan Jihar, Ikenga Tochukwu, wanda ya yi magana da yan jarida a ranar Laraba 17 ga watan Agusta ya tabbatar da kama Iloka, The Nation ta rahoto.
Tochukwu ya bayyana cewa an kama Iloka ne kan zargin yana da hannu a mutuwarsa, Chidiebere.
Amma, jami’in mai magana da yawun yan sandan ya ce, sashin binciken manyan laifuka na rundunar, SCID, har yanzu tana bincike kan abin da ya faru.
Source: LEGITHAUSA