Tsohon Wazirin Katsina, Farfesa Abubakar Sani Lugga, ya yi kira ga sarakuna domin Allah shugabannin addinai da ba za su iya fadawa shugabanni gaskiya ba da su yi murabus ko a tsige su.
Lugga ya yi bayanin cewa abubuwa na kara tabarbarewa a Najeriya duk da yawan addu’a da al’ummar kasar ke yi a kullun saboda kasar na karkashin la’antar Allah Har ila yau, ya kuma kafa hujja da Al-Kur’ani mai girma da littafi mai tsarki domin tabbatar da ikirarin nasa.
Tsohon Wazirin Katsina, Farfesa Sani Abubakar Lugga ya bayyana cewa abubuwa na ci gaba da tabarbarewa a Najeriya duk da addu’o’in da al’ummar kasar ke yi a kullun saboda kasar na karkashin la’antar Ubangiji.
Farfesa Lugga ya ce hakan ya faru ne sakamakon rashin shugabanci nagari, yana mai jan ayoyi daga Al’kur’ani mai giema da littafi mai tsarki.
Wazirin Katsina na biyar ya yi wannan martanin ne a gidansa yayin da yake zantawa da wasu manema labarai a daren ranar Juma’a, jaridar Vanguard ta rahoto.
Daga cikin kokarin sauya wannan lamari, Farfesa Lugga ya shawarci sarakuna da shugabannin addinai wadanda ke tsoron bayar da shawarwari na gaskiya ga shugabannin siyasa da su yi murabus ko kuma a tsige su don ba wadanda za su iya aikin yadda ya kamata dama, rahoton Daily Post.
Wani bangare na jawabin Lugga na cewa: “Yanzu haka, muna a cikin tsarkakken lokaci inda Musulman Najeriya ke a Makka don aikin Hajji sannan Kiristocin Najeriya na a Jerusalem suna gudanar da aikin Hajjin Ista.
“Gwamnatin tarayya ta ayyana hutun Sallah, inda ta bukaci Musulmai da su yi addu’an zaman lafiya tsaro da ci gaban Najeriya.
“Majalisar harkokin Musulunci da duk sauran kungiyoyin Musulunci sun bukaci ayi addu’a. “Kungiyar Kiristocin Najeriya da sauran kungiyoyin kiristanci sun yi kira ga addu’o’i. shugaban kasa, gwamnoni, sarakunan gargajiya da shugabannin addinai sun yi kira ga addu’o’i.
“Amma, shin wadannan shugabanni da dukkanin yan Najeriya sun damu da tambayar dalilin da yasa abubuwa ke kara tabarbarewa a kasar da ke cikin addu’a a kullun? Amsar mai sauki ce: Najeriya na fuskantar Najeriya na fuskantar la’anar Allah.
“Ayoyi da daman a Al-Qur’ani mai girma da koyarwar Annabi Muhammad (SAW) da ayoyin injila da dama da koyarwar Almasihu sun goyi bayan wannan hasashen.
“Alkur’ani mai girma yana cewa: ‘Ya ku mutane! La’anar Allah ta tabbata a kan wadanda suka aikata ba daidai ba! (Qur’an 11:18). “Littafin Injila ya ce, ‘La’ananne ne duk wanda ba ya kiyaye dukan abin da aka rubuta a littafi mai tsarki, ya aikata su.
“Har ila yau, Alkur’ani mai girma yana cewa: ‘Lallai Allah ba zai canza halin da mutane suke ciki ba matukar ba su canza yanayinsu harkokinsu da kansu ba. (Kur’an 13:11).
“Kuma Littafi Mai Tsarki ya ce, ‘Imani da kansa, idan ba a bisa da aiki ba, matacce ne. (James 2:17). “Alkur’ani mai girma yana cewa: “Mu tashi daga cikinku wasu jama’a suna kira zuwa ga abun da yake alheri, suna umarni da kyakkyawan ayyuka sannan kuma suna hani da abun da yake mummuna. (Qur’an 3:104).”
A wani labari na daban, mun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya amince da daukar Musulmi a matsayin abokin takararsa gabannin babban zaben shugaban kasa na 2023.
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 8 ga watan Yuli, a yayin bikin babban Sallah a jihar, Daily Independent ta rahoto.
Tinubu ya dauki Alhaji Kabir Ibrahim Masari, dan siyasar Katsina, a matsayin mataimaki na wucin gadi domin cike wa’adin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta diba masa.