Bayanan da aka samu a ‘yan kwanakin nan na nuna akwai karancin alkalai da mayan ma’aikata musamman a manyan kotuna kassar nan, Kotun Koli da Kotun Daukaka Kara.
Rahotanni sun bayyana cewa, karancin alkalai a Kotun Koli ya bayyana ne bayan ajiye aikin da Maishari’a Amina Adamu Augie, da Maishari’a Mary Odili wadda ta yi ritaya kafin ita da kuma rasuwar Maishari’a Centus Chima Nweze. Rahoton ya kuma nuna cewa, a halin yanzu alkalai 11 suka rage maimakon alkalai 21 da doka ta tanada. Wannan lamarin yana matukar nakasa ayyukan masu shari’a saboda yawan aikin da ke gaban su hakan kuma yana shafar kokarin su na sauke nauyin yanke hukunce-hukunce a shari’un da ke gaban su.
Karin matsalar kuma a nan shi ne a cikin alkalai 11 da suka rare a kotun kolin 7 daga cikin su za su shiga aikin sauraran daukaka karar da da ‘yan takarar shugabancin kasar nan Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar LP sai kuma jam’iyya APM wadanda suke kalubalantar nasarar da dan takarar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu a zaben da aka yi a shekarar 2023 wanda kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta tabbatar masa da nasara kwanakin baya.
Haka ya zama saura alkalai 4 kenan da za su fuskanci dinbin kararrakin da ke gaban Koton Kolin ciki har da kararrakin zaben gwamnoni wanda shi ma sai ya dangana da Koton Koli don yanke hukunci.
Hukumar Kula da Harkokin Shari’a (NJC) ce ke da alhakin amincewa da wadanda za a nada a matsayin alkalai a Koton Kolin daga na sai shugaban kasa ya mika sunayen su ga majalisar dattawa don su tabbatar da su, aikin su ne yanke hukunci a kan matsalolin da sukan taso a tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi da kuma matsalolin da ke tasowa a tsakanin jiha da jiha da sauran rikice-rikice a tsakanin al’umma.
Shugabanin manyan kotuna biyu na kasa sun koka a kan yadda aiki ya yi musu yawa da kuma karancin alkalai da za su fuskanci ayyukan. A jawabinsa kwanakin baya lokacin da ake rantsar da alkalai 9 da za su yi aiki a kotun daukaka kara, alkalain alkalan Nijeriya, Maishari’a Olukayode Ariwoola, ya koka a kan yadda shari’un zabe suka cika kotunanmu, ya ce, suna matukar takura alkalai, aikin kuma yana yi musu yawa kwarai da gaske, in ji shi.
A watan Nuwamba na shekarar da ta gabata, a yayin rantsar da sabbin manyan lauyoyi 62 na kasa a Abuja, alkalin alkalan Nijeriya Ariwoola ya jaddada cewa, bincdike ya nuna cewa Koton Kolin Nijeriya ce tafi duk wata kotun koli a duniya yawan ayyuka, wanan yana nuna irin aiki tukurun manyan alkalan Nijeriya.
A yayin da ake shari’u fiye da 6,884 kuma gashi alkalan da za su saurari wadanna shari’un suna kara raguwa, lallai za a iya samun matsalar dadewa shari’u, wanda kuma dadewar shari’a tamkar rashin aldalci ne ga masu neman hakkinsu.
Rahotanni sun nuna cewa a bayan zaben shekarar 2023 manyan kotunan tarayya sun karbi kararraki fiye da 3,000 wadanda ake sa ran za su bi ta kutunnan daukaka kara har zuwa Koton Koli don warwarewa.
Haka kuma shugabar kotun daukaka kara, Mai shari’a Dongban-Mensem, ta yi bayani kamar yadda alkalin alkalan Nijeriya ya yi a yayin kaddamar da shekarar shari’a ta 2023/2024.
Ta ce, kutun na da kararraki fiye da 39,526 wadanda suka rarraba a bangarorin kotun 20 sun kuma hada da kararrakin zabe. Maishari’a Dongban-Mensem ta bayyana cewa, bayan babban zaben 2023 sun kafa kotunan zabe 98 da za su duba shari’u 1,209 da ‘yan takarar zabe suka mika wa kotunan a jihohi daban daban.
Ta bayyana damuwar ta a kan yadda shari’un zabe suka cika kotunan Nijeriya wanda hakan na nufin cewa, sauran matsaloli da suka shafi rikice-rikicen filaye, hakokin dan adam, matsalar kasuwanci da sauran rikice-rikice za su ci gaba da zama a kotuna na tsawon lokaci.
Alkali alkalan Nijeriya, Ariwoola da shugabar kotun daukaka kara, Dongban-Mensen sun yi kira da cewa, bai kamata a ce dukkan shari’un zabe sai sun dangana ga kotuna ba, ya kamata a rinka neman hanyar warware rikice -rikicen zabe musamman ganin yadda kotuna suka cika da shari’u da ke bukatar a funskance su a kotunanmu.
Yana kuma da matukar muhimmanci a a kafa kotuna na musamman don sauraron kararrakin zabe kamar yadda kungiyar lauyoyi ta kasa ta yi kwanakin baya, a kan haka kuma muna kira ga Hukumar Kula da Harkokin Shari’a NJC ta mika sunayen wadanda ya kamata a nada a mastayin alkalan Koton Koli kamar yadda dokar kasa ta 230(1) (B) na kundin tsarin mulkin Nijeriya ya samar, ya kuma kamata a samar da isassun ma’aikata a kananan kotunan kasar nan don aiki a kan shari’un da ke gabansu kamar yadda ya kamata, kuma kan lokaci.
Source: LEADERSHIPHAUSA