Alhazan babban birnin tarayya Abuja na fuskantar wahalhalun da ba za a iya fada ba a kasar Saudiyya, sabida rashin samun kyawawan masaukai.
Bincike ya nuna cewa, wasu daga cikin mahajjatan a rukunin farko a kasar Saudiyya sun koka sosai kan cewa, masaukansu ba su cika sharada na mafi karancin ababen more rayuwa ba da kwamitin tsare-tsare na aikin Hajji ya tanada.
Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa Daraktan Hukumar Jin Dadin Alhazai na FCT, Malam Abubakar Evuti, ya nuna gazawa wurin iya shugabanci.
Jaridar New Telegraph ta tattaro cewa, Hukumar Alhazai ta kasa ta ware kujeru 3,562 ne kawai ga FCT, amma hukumar ta FCT ta yi aringizon kujeru har sama da 4,000.
A wani labarin na daban babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙaryata batun cewa ya karya darajar Naira inda Dala 1 ta koma Naira 630.
CBN ya ce labarin da Jaridar Daily Trust ta bayar ba gaskiya ba ne, tunani ne kawai irin nasu.
Bankin ya ce ko a yau da safe ana sayar da Dala 1 a kan Naira 465 a kasuwar canjin kuɗi na gwamnati.
Don haka bankin ya yi kira ga ‘Yan Nijeriya su yi biris da labarin saboda ba shi da tushe balle makama.