Alfanun sauya fasalin takardun naira na da yawa sosai – CBN.
Babban Bankin Najeriya na CBN ya ce akwai alfanu sosai game da sauya wa wasu daga cikin takardun naira fasali, waɗanda ya ƙaddamar a yau Laraba.
Cikin jawabin da Gwamnan CBN Godwin Emefiele ya gabatar yayin bikin, ya ce daga cikin alfanun da za a samu har da daƙile yunƙurin buga jabun kuɗi.
“Alfanun da za a samu na sauya fasalin naira na da matuƙar muhimmanci ganin cewa yunƙurin zai taimaka wajen rage hauhawar farashi ta hanyar mayar da kuɗi zuwa bankuna,” in ji shi.
“Kazalika, zai tallafa wajen gyara fasalin kuɗin da kuma samun cikakkun bayanai game da zagayawar kuɗi a tsakanin jama’a.
“Mun yi imanin cewa hakan zai jawo ƙaruwar jama’a cikin harkokin kuɗi da kuma rage amfani da garin kuɗin.
“sauya fasalin zai taimaka wajen yaƙi da rashawa saboda za a ƙara saka wa manyan takardun naira ido waɗanda su kuma za a iya bin sawunsu daga bankuna cikin sauƙi.”
Read More :
An kashe mutum 422 a jihohin Najeriya uku cikin wata ɗaya – Rahoto.
Bincike: Shin Bidiyon da Ya Karade Soshiyal Midiya na Sabbin Takardun Naira ne?
Mutum 17 sun mutu a hadarin mota kan hanyar Abuja.