Gwamnatin Nijeriya za ta kaddamar da wani kwamiti mai wakilai 37 da zai aiki kan mafi karancin albashin ma’aikata na kasa da bayar da shawarwari kan karin mafi karancin albashi a Nijeriya.
Wata sanarwa da daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Segun Imohiosen, ya fitar, ya bayyana cewa kaddamar da kwamitin na cikin umarnin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar na kafa shi.
A cewar sanarwar, Bukar Goni Aji, tsohon shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ne zai shugabanci kwamitin da mambobinsa daga gwamnatin tarayya da gwamnatin jihohi da kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin kwadago.
Sanarwar ta ce, “Daga bangaren Gwamnatin Tarayya, mambobin sun hada da Nkeiruka Onyejeocha da Karamin Ministan Kwadago da Aiki, Hon. Wale Edun da Ministan Kudi.
Sauran ‘yan kwamitin sun hada da “Ministan Tsare-tsaren da Kasafin Kudi Atiku Bagudu da shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya Yemi Esan da kuma Babban Sakatare, GSO. OSGF, Nnamdi Maurice Mbaeri da Ekpo Nta, shugaban NSIWC a matsayin Sakatariya.
“Haka kuma daga bangaren gwamnatin jiha, gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ne zai wakilici gwamnonin Arewa ta tsakiya sai gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, a matsayin wakilin jihohin Arewa maso Gabas da Alh. Umar Dikko Radda, Gwamnan Jihar Katsina, a matsayin wakilin Arewa maso Yamma, sauran sun hada da Charles Soludo, gwamnan jihar Anambra, a matsayin wakilin yankin Kudu maso Gabas, sai kuma Sanata Ademola Adeleke, Gwamnan jihar Osun a matsayin wakilin yankin Kudu maso Yamma, sai gwamna jihar Cross River, Otu Bassey Edet a matsayin wakili daga Kudu maso Yamma.
“Daga kungiyar tuntubar ma’aikata ta Nijeriya (NECA) – Adewale-Smatt Oyerinde, Darakta-Janar na NECA da Chuma Nwankwo da Thompson Akpabio tare da mambobi daga Kungiyar ‘yan Kasuwa, Masana’antu, Ma’adinai da Noma ta Nijeriya (NACCIMA) wadanda suka hada da Shugaban kasa, Asiwaju (Dr) Michael Olawale-Cole da Hon. (Dr) Ahmed Rabiu, Mataimakin Shugaba kuma Babban jami’a a Humphrey Ngonadi (NPOM).”
Sanarwar ta kara da cewa mambobin kwamitin sun hada da kungiyar masu kananan sana’o’i ta kasa (NASME) su ne Abdulrashid Yerima, Shugaban Majalisar, sai Theophilus Nnorom Okwuchukwu, wakilin kamfanoni masu zaman kansu; Dr. Muhammed Nura Bello, a matsayin mataimakin shugaban daga shiyyar arewa maso yamma.
Kazalika, daga kungiyar masu ‘yan kasuwa ta Nijeriya (MAN) akwai Misis Grace Omo-Lamai, Daraktar Ma’aikata ta Kamfanin Breweries ta Nijeriya; Segun Ajayi-Kadir da Darakta-Janar, MAN; Lady Ada Chukwudozie da Manajan Darakta, Dozzy, a bangaren Oyal da iskar gas.
“Daga kungiyar kwadago, kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) Kwamared Joe Ajaero, shugaban kungiyar NLC da Kwamared Emmanuel Ugboaja da Kwamared Prince Adeyanju Adewale da Kwamared Ambali Akeem Olatunji da Kwamared Benjamin Anthony da Farfesa Theophilius Ndukuba.
“Kazalika, mambobin kwamitin daga kungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya (TUC) sun hada da shugaban kungiyar TUC, Kwamared (Engr) Festus Osifo da Mataimakin Shugaban TUC, Kwamared Tommy Etim Okon da Kwamared Kayode Surajudeen Alakija, mataimakin kungiyar ta kasa .na II da Kwamared Jimoh Oyibo, mataimakin shugaban kasa na III, sai Kwamared Nuhu A. Toro, Sakatare Janar da Kwamared Hafusatu Shuaib, shugabar mata ta Women Comm,” cewar sanarwar.
Source: LEADERSHIPHAUSA