Al’ajabi Yadda wata mata haifi ‘yan biyu daya mutum daya maciji a Jihar yobe.
Daga: Muhammad Inuwa Zariya
“Majiyar Alfijir Hausa ya kawo mana rahoton cewa, a jahar yobe cikin wata karamar hukuma ta guro macina, Allah ya saukar da wani abun al-ajabi “inda wata mata da ake kira da babar bariya ta haifi wasu ‘yan biyu daya mutum daya maciji.”
“Rahoton ya cigaba da bayyana jaridar cewa cewa, inda aka radama dayan jaririn suna Abubakar, “inda ya zama babban sarki anan masarauta na macina, shi Kuma macijin yakoma kan dutsan juwa da rayuwa a tun wancan lokacin.”
“Sai dai abun mamaki shine, duk wani hidima idan ana yi a gidan na sha’ani, shima macijin yakan halarta wannan waje Kuma ba yayima kowa komai da sunan cutarwa har a gama taro.”
“Sai dai idan kaje garin a halin yanzu haka, za kaga tarin macizai bila adadin suna rayuwa cikin mutane, amma Kuma ba’a kashe su sabo da basayima kowa komai.”
Bayanin bai tsaya ba, inda rahoton ya cigaba da cewa, sai dai a wani lokaci a baya, wani gardi yataba kashe macijin guda daya a bisa rashin sani saboda yaje gona inda ya kona gonanshi Ashe maciji daya na ciki aiko wutannan ya konashi kurmus.”
“Inda hakan ya kawo konewar garin baki daya, shi kuma ya gudu, Amma a yanzu haka suna rayuwa da al-ummah babu wata matsala suna yawan Kai gaisuwa gidan sarautan gidan, Kuma idan ana biki agidan sarkin macina suna zuwa sabo da kakansu shima Dan sarki ne.”