Alkalin babban kotun tarayya a Abuja ya fara karbe wasu daga cikin kadarorin Akanta Ahmad Idris.
Kudin da Hukumar EFCC za ta raba tsohon Akanta Janar da su, sun kunshi N300m da wasu.
Daloli Akwai kadarori a garuruwan Abuja da Kano da Alkali ya ce EFCC ta karba kafin gama shari’a.
Babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja ya umarci a karbe wasu miliyoyi da daloli da kuma kadarorin da Ahmed Idris yake ikirarin ya mallaka.
A rahoton Vanguard na ranar Laraba, 21 ga watan Disamba 2022, an ji cewa gwamnatin tarayya za ta karbe $899,900 da N304.5m daga hannun tsohon jami’in.
Akanta Ahmed Idris wanda ya rike kujerar Akanta Janar kafin a dakatar da shi kwanakin baya, zai sallama wasu gidaje da kadarori da ya mallaka a birnin Abuja da Kano.
A yau ne aka ji labari Alkali M.A Hassan ya zartar da wannan hukunci da yake sauraron kara mai lamba HC/CR/299/2022 da lauyoyin hukumar EFCC suka gabatar.
Ana so a raba tsohon AGF da dukiyarsa Lauyoyin da suka tsayawa EFCC a gaban kotun kasar su na so dukiyar da Idris Ahmed ya mallaka su koma hannun gwamnati kafin lokacin da za a karkare shari’a.
A madadin EFCC, Monyei Samuel Ekene ya zabi kotu ta bada umarni a rufe asusun bankin wanda ake tuhuma, sannan a karkatar da ribar da ake samu daga ajiyar.
Za a bude akawun na musamman a banki inda za a tattara abin da aka rika samu na riba daga wadannan asusun banki da hukuma ta bada umarnin a karbe.
Gidaje, filaye da shaguna su na cikin kadarorin da EFCC za ta karbe zuwa lokacin da Alkali zai gama sauraron shari’ar da ake yi da tsohon Akanta Janar din.
Rahoton ya ce Mai shari’a Hassan ya amince da bukatar Lauyan masu kara, tare da wasu sharuda.
An karbe shagon Mall/Al Ikhlas Shopping Mall a Mandawari da wani bene da shaguna a Ladanai a Kano, kuma akwai gida a unguwar Karsana a birnin Abuja.
Ragowar gidajen su ne Royal Duplex a Daneji da ke garin Kano da wani katafaren gida da ke kan titin New Jersey a rukunin Efab Blue Fountain duk a garin Abuja.
Shekaru 300 a kurkuku Kun ji labari cewa satar N34m ta jawo wani Akanta da aka yi a FCE Eha-Amugu a garin Isi-Uzo a jihar Enugu, zai yi fiye da shekaru 300 yana garkame a gidan yari.
Tun a 2010 ake shari’a tsakanin Emmanuel Sombo da Lauyoyin EFCC a kan zargin ya saci Naira Miliyan 34.5 daga asusun makaranta, sai yanzu aka iya gama shari’ar.