Shugaban kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC), Joe Ajaero ya bayyana irin halin da ya shiga a hannun ‘yansanda bayan da aka kama shi a Owerri, jihar Imo.
Ajaero ya ce tabbas Allah ne ya sa yana da kwana a gaba saboda dukan da ya sha a hannun ‘yansanda.
Idan za a tuna cewa ‘yansanda a jihar sun ce bata gari sun shirya tarwatsa zanga-zangar NLC a Owerri, babban birnin jihar Imo.
Shugaban NLC ya je garin Owerri ne domin tara ma’aikatan Imo domin gudanar da zanga-zanga a jihar kan cin zarafin ma’aikata da yake zargin gwamnatin jihar na yi.
Rikicin da ya barke a yayin gangamin ya kai ga jami’an ‘yansandan Nijeriya yin awon gaba da Ajaero.
Da yake magana bayan an sake shi, Ajaero ya ce ‘yansanda sun yi barazanar kai shi kotu.
A cewar Ajaero: “Idan ka ce odar wucin gadi, to, za ta wuce a sannu; idan kotu ce ta fitar da odar, to wani abu ne na daban. Na ce musu odar wucin gadi na karewa cikin mako daya ko biyu; sai suka ajiye takardar suka ce min za su iya gurfanar da ni.
“Na fada musu cewa kotu ce kadai za ta iya gurfanar da mutum; ba za su iya gurfanar da ni ba.
“Sun dake ni; tabbas Allah ne Ya yi ina da sauran kwana a gaba.”
Source: LEADERSHIPHAUSA