Hon. Bashir Machina ya ce duk da mutanen Lawan su na tuntubarsa, ba zai hakura da tikitinsa ba ‘Dan siyasar ya koka a kan Ahmad Lawan, yake cewa.
Bashir Sheriff Machina wanda ya lashe tikitin APC na Sanatan Arewacin Yobe, ya yi hira da Punch a kan tirka-tirkar da ake yi a jihar Yobe.
Hon. Bashir Sheriff Machina ya yi karin-haske a kan dalilinsa na kin janye takararsa ga Ahmad Lawan wanda shi ne shugaban majalisar dattawa.
A cewar Bashir Sheriff Machina, ba maganar cancanta ake yi ba, mutanen Yobe ta Arewa sun gaji da wakilcin Lawan wanda ya yi Sanata sau hudu.
Jam’iyyar APC A shekara mai zuwa, Lawan zai cika shekara 16 a majalisar dattawa, Machina yake cewa mutanen yankinsa su na neman sabon ‘dan majalisa. Sheriff ba kanwar lasa ba ne a siyasa Machina ya bayyana cewa tun 1992 ya zama ‘dan majalisar wakilan tarayya a karkashin jam’iyyar SDP, a lokacin yana ‘dan shekara 26 da haihuwa.
Daga 1999 zuwa yanzu, jagoran na APC a yau yake cewa ya taba zama Mai ba Atiku Abubakar shawara a kan harkar siyasa, a lokacin su na mulki.
Hon. Bashir Sherrif Machina Hoto: muhammed.alhajigarba.90 Asali: Facebook Haka zalika Machina ya ce ya rike mukamai a jam’iyyun adawa na AC da PDP, ya kuma tabbatar da ana ta faman rokonsa ya yafe tikitinsa na APC.
Tsohon ‘dan majalisar ya ce ya yi aiki da Tinubu a AC, don haka ba zai taba cin amanarsa ba. Sannan ya kuma tabbatar da cewa zai je gaban Alkali.
Al’umma sun gaji haka – Machina ‘Dan takaran ya yabi Gwamnan Yobe, Mai girma Mai Mala Buni, wanda ya ce bai nuna son kai a kan batun takarar Sanata na yankin Arewacin jihar ba.
An rahoto ‘dan takaran yana cewa ba zai sulhunta da Lawan ba, domin mutanen Arewacin jihar Yobe sun gaji da wakilcin shugaban majalisar dattawan.
“Babu abin da zan iya yi masa illa in fada masa ya hakura da burinsa saboda ra’ayin jama’a. Mutanensa su na neman canji, sun gaji da shi, don haka sai ya je ya huta.”
Tinubu ya yi caca a APC Ku na da labari Asiwaju Bola Tinubu ya ba INEC sunan Kabir Ibrahim Masari mr, amma da zarar a tsaida ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa, za a canza shi.
Abdulazeez Yinka-Oniyangi wanda Shugaban kamfe ne a Arewa maso tsakiya ya ce APC ba ta da matsala saboda ta dauki Tinubu da wani musulmi a zaben 2023.