Rundunar yan sandan Jihar Adamawa ta kama wata Caroline Barka kan zarginta da kashe mijin ta.
Dauda Barka Caroline ta shaida wa yan sanda cewa ta daba wa mijinta wuka ne saboda ba shi da aiki kullum sai shan giya da yawon dare Sikiru Akande, kwamishinan yan sandan jihar ya bada umurnin a gudanar da sahihin bincike da nufin a gurfanar da wacce ake zargin a kotu.
Wata mata yar shekara 20 mai suna Caroline Barka, ta kashe mijinta, Dauda Barka, a Barkam Jihar Adamawa a ranar Juma’a a cewar yan sanda, The Nation ta rahoto.
A cewar rundunar yan sandan, Caroline ta daba wa mijinta mai shekara 38 wuka ne a Tsamiya a garin Madagali na Jihar.
Ta bayyana cewa mijinta yana yawon dare kuma yana shan giya, wanda ta ce hakan na haifar da matsala ga walwalar iyalansa.
Ta ce a ranar, mijinta ya dawo gida cikin dare kuma ya fada kan jinjirinsu. Martanin yan sanda kan lamarin SP Suleiman Nguroje, kakakin yan sandan jihar, ya tabbatarwa manema labarai lamarin a jiya.
Nguroje ya ce: “An yi jayayya tsakanin mata da mijin bayan mijin ya dawo gida cikin dare kuma tatul da giya. Rundunar yan sandan Jihar Adamawa a ranar 22/7/2022 ta kama matar aure yar shekara 20 kan caka wa mijinta dan shekara 38 wuka har ya mutu.
“Wacce ake zargin, Caroline Barka, wacce ke zaune a Angwan Tsamiya, karamar hukumar Madagali, fara jayayya da marigayin mijinta, Barka Dauda, bayan ya dawo cikin mayen giya ya fadi kan yaronsu dan shekara daya da ke barci a gado.
“Saboda fushin shan giyansa da yawon dare da rashin kula da iyalansa a matsayin miji, wacce aka zargin ta kama shi da dambe da caka wa mijin wuka, sakamakon hakan ya fadi summame kuma daga bisani aka garzaya da shi asibiti inda aka tabbatar ya rasu.
“Yan sanda sun kama wacce ake zargin bayan dan uwansa ya kai korafi. Bincike kawo yanzu ya nuna wacce ake zargin tana shayarwa ne kuma shekarunsu biyu da aure da mammacin.”
Nguroje ya ce kwamishinan yan sandan jihar, Sikiru Akande ya bada umurnin a gudanar da sahihin bincike kan lamarin da nufin ganin an gurfanar da wacce ake zargin an kuma hukunta ta.
Babban Magana: An Kama Marubuciyar Littafin ‘Yadda Za Ki Kashe Mijinki’ Da Laifin Kashe Mijinta.
A gefe guda, wannan labarin na iya kama da shirin fim, amma da gaske ne, inda wata kotun Amurka ta kama Nancy Brophy – wata marubuciyar wani littafi, ‘Yadda Za Ki Halaka Mijinki’ – dumu-dumu da laifin halaka mijin ta.
Source:hausalegitng