Kwamitin Likitoci mai zaman kansa na kasar Sudan ya ce akasarin adadin mutanen da suka mutu harbe su aka yi da bindiga.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Duniya IOM, ta ce tashe-tashen hankulan sun raba mutane fiye da dubu 83,000 da muhallansu.
A shekarar 2003 yakin basasar ya barke a yankin Darfur tsakanin sojojin gwamnati, da wasu adadin ‘yan tawayen kabilu marasa rinjaye, wadanda suka yi korafin ana nuna musu wariya, a karkashin gwamnatin tsohon shugaba Omar al-Bashir.
Aikin dakarun Majalisar Dinkin Duniya na wanzar da zaman lafiya a Darfur dake Sudan ya kare a wannan Alhamis 31 ga watan Disamba, a yayin da al’ummar yankin ke cike da fargabar sake barkewar sabon tashin hankali, sakamakon rikice-rikicen kabilancin da suka fuskanta a baya bayan nan.
Akalla mutane dubu 300 ne suka rasa rayukansu a tsawon shekarun da aka shafe ana gwabza yakin, yayin da wasu miliyan 2 da dubu 500 suka rasa muhallansu, kamar yadda alkaluman majalisar dinkin duniya suka nuna.
Rikicin na Darfur dai yayi sauki matuka a shekarun baya bayan nan, zalika a shekarar bara sojoji suka kawar da gwamnatin shugaba al-Bashir da kotun duniya ICC ke nema bisa tuhumarsa da aikata laifukan yaki a yankin na Darfur dake yammacin Sudan.
Sai dai wasu sun bayyana shakku kan ko gwamnatin rikon kwaryar kasar za ta iya karbar aikin tabbatar da tsaron yankin na Darfur, la’akari da rikice-rikicen kabilancin da har yanzu kan tashi, ciki har da wanda aka kashe mutane 15 a makon jiya, lamarin da ya sanya wasu daruruwan al’ummar yankin gudanar da zanga-zangar adawa da ficewar dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya.