Adadin mutanen da suka mutu a gobarar dajin Amurka na ƙaruwa cikin sauri
An tabbatar da mutuwar mutum 93 sakamakon gobara a tsibir Maui wadda ta ƙone garin Lahaina mai ɗumbin tarihi.
Gobarar ta kasance mafi muni a tarihin Amurka cikin ƙarni ɗaya.
Yayin da ake ci gaba da tantance waɗanda ibtilain gobarar ya shafa, a ranar Asabar Gwamnan Hawaii Josh Green ya yi hasashen ƙaruwar adadin waɗanda suka mutu.
Ɗaruruwan mutane sun yi ɓatan dabo yayin da wasu da dama suka tsere wa gidajensu a Maui.
“Rana ce ta tsananin tashin hankali,” a cewar Mista Green. “Wannan gobara “bala`i ne da al’ummar Hawaii suka fuskanta”.
“A yanzu za mu mayar da hankulanmu kan waɗanda suka tsira, za mu yi aikin sada iyalai da ‘ƴan uwansu da suka ɓace sannan mu samar musu da gidajen zama na wucin-gadi da magunguna kafin mu sake gine-gine.”
Hukumomin yankin sun ci gaba da aikin laluben waɗanda ɓaraguzan gine-gine suka danne ta hanyar amfani da karnukan da aka bai wa horo na musamman don gano inda mutum yake a binne.
Babban jami’in ‘yan sanda a Maui, John Pelletier, ya ce sun yi nasarar tono kashi 3 na yankin da ake zaton akwai mutane binne.
“Tilas a yi wa mutane gwajin ƙwayoyin halitta don tantance su, domin kowa daga cikin waɗannan mutane 93 sunansa John ko Jane Doe”, cewar shugaban ‘yan sandan.
Jami’in hukumar agajin gaggawa Jeremy Greenberg,ya shaida wa BBC cewar sun samu gudummawar ƙarin taimakon jami’an kashe gobara da ƙwararru a aikin neman waɗanda suka ɓace.
“Muhimmin abu shi ne tsaro da lafiyar waɗanda suka tsira,” in ji jami`in.
Mista Greenberg ya ƙara da cewar akalla mutum 1,000 suka yi ɓatan dabo, ɗaruruwan mutane sun tsira amma sun ƙi fitowa su bayyana kansu saboda wasu dalilai.
Ɗaruruwan mutanen da suke matsugunan gaggawa da mahukunta suka yi tanadi a cibiyar tunawa da dakarun da suka sadaukar da kawunansu a yaƙi da ke Maui sun samu abinci da magunguna bayan da aka samu masu aikin agajin gaggawa na sa-kai.
Keapo Bissen, mamba a cibiyar, ta ce ana samun ƙaruwar adadin wadanda suka ɓata, a kowacce s’a iyalai na kawo rahoton ɓatan ‘ƴan uwansu.
”Abin farin ciki ɗaya shi ne, lokacin da iyalai suka haɗu da ɗan uwansu da ya bace ,” a cewarta.