Adadin mutanen da aka kashe a jerin hare-haren da ‘yan bindiga suka kai jihar Filato da ke tsakiyar Nijeriya ya karu zuwa kusan 200, kamar yadda hukumomi suka bayyana ranar Laraba, a yayin da aka soma binne wadanda suka mutu.
Wasu ‘yan bindiga da kawo yanzu ba a san ko su wane ne ba sun kaddamar da jerin hare-hare a kauyuka kusan ashirin a jihar ta Filato ranar Asabar da maraice da kuma Talata da safe.
Tun da fari, hukumomi sun ce mutum 163 ne suka mutu a hare-haren da aka kai a kananan hukumomin Barkin Ladi da Bokkos.
Sai dai yayin da mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya kai ziyara a jihar ta Filato ranar Laraba, shugaban karamar hukumar Bokkos Monday Kassah ya ce mutum 148 aka kashe a yankinsa.
Kazalika an kashe mutum akalla 50 a kauyuka daban-daban na karamar hukumar Barkin Ladi, a cewar Dickson Chollom, wani dan majalisar dokokin jihar daga yankin.
“Muna rokonku da ku guji raba kawuna da kiyayya ga junanku, a yayin da muke kokarin ganin an yi adalci domin samar da zaman lafiya,” in ji Kashim Shettima a yayin da ya gana da jami’an gwamnati da sarakuna da kuma mazauna yankunan.
Ana fargabar cewa alkaluman mutanen da suka mutu ka iya karuwa domin kuwa har yanzu akwai wadanda suka bata, a cewar Kassah a hira da kamfanin dillancin labarai na AFP ranar Talata, inda ya kara da cewa an jikkata mutum 500 sannan an raba dubbai da gidajensu.
‘A kama wadanda suka aikata laifin’
An binne mutane da dama ranar Talata, inda mataimakin shugaban majami’ar Church of Christ in Nations, Timothy Nuwan, ya ce wadanda aka binne sun kai 150.
“An kashe adadin mutane da dama, wasu an yanka su kamar dabbobi, yayin da aka kona wasu a cikin gidajensu da kuma a waje,” in ji shi.
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ranar Talata ya yi tir da hare-haren sannan ya umarci “jami’an tsaro su yi gaggawar shiga yankuna da kuma kama wadanda suka aikata laifin”.
Gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang ya yi kira “a hada gwuwa domin gano wadanda suka aikata wannan danyen-aiki”.