‘Yan takara fiye da 400, daga jam’iyyun siyasa 14 ne suke takarar neman kujerun Camomi da kansiloli a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja a yau Asabar.
Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa shiyoyin da ake zaben sun hada da Abaji, Bwari, Gwagwalada, Kuje, Kwali da Abuja Municipal (AMAC). Sannan za’a zabi camomi 6 da kanciloli 62 ne a dukkan shiyoyin guda 6. Har’ila yau mutane kimani miliyon 1.3 suka cancanci kada kuri’unsu a cibiyoyin zabe 2,229 a duk fadin birnin Abuja a zaben na yau Asabar.
Masana suna ganin manya-manyan jam’iyu guda biyu na kasar wato PDP da kuma APC ne zasu mamaye zaben, saboda sune suke kan wadannan kujeru tun zaben shekara ta 2019. Sauran jam’iyyun da wuya su tabuka wabi abu a zaben na yau.
A halin yanzu dai jam’iyyar APC mai mulkin kasar ce take rike da shiyoyi 4, Abaji, Kwali, Gwagwalada da kuma Municipal a yayin da PDP take rike da Kuje da Kwari.