Kotun daukaka kara a Abuja ta bai wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da Peter Obi na jam’iyyar LP damar duba kayayyakin da aka yi amfani da su a zaben ranar 25 ga watan Fabarairu.
Tun farko ‘yan takarar ne daban-daban suka mika bukatar neman a ba su damar duba kayayyakin da aka yi amfani da su a babban zaben 2023 tare da tilasta wa INEC ta ba su damar ganin kayan aikin da aka yi amfani da su a zaben shugaban kasa.
A ranar Laraba ne Atiku ya shigar da tasa karar yayin da Peter Obi kuma ya shigar da tasa ranar Alhamis.
Kan haka ne kotun dake zaman ta a Abuja ta umarci INEC ra ta bai wa dan takarar PDP damar duba kayayyakin zaben.
A yau Juma’a kuma kotun ta amsa bukatun ‘yan takarar na duba kayan zaben sannan kuma su titsiye hukumar zabe kan wasu bayanai da za su bukata.
Kotun karkashin mai shari’a Joseph Ikyegh ta bayar da umarnin ne bayan da ta saurari wasu kararraki da ‘yan takarar biyu suka shigar tare da jam’iyyunsu.
PDP da LP wadanda a baya-bayan nan suka yi watsi da sakamakon zaben, sun ce samun damar ganin kayayyakin za ta taimaka musu a kalubalantar sakamakon zaben da suke yi wanda ya ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara.
A cewar INEC, Tinubu ya lashe zaben ne da kuri’u 8,794,726, yayin Atiku ya samu kuri’u 6,984,520 sai Obi na Labour Party da ya zo na uku da kuri’u 6,101,533.
Source:Leadershiphausa