Jiga-jigai a sanin fannin siyasa da lamurran kasa sun yi hasashe sun ce ana iya samun matsala a APC da LP Ganin yadda jam’iyyun suka zabo abokan takarar, masana sun yi maganganu kan matsalolin da za a iya samu.
Jam’iyyar APC da LP ne suka zabo ‘yan takarar da ake sa ran na wucin gadi ne, wanda ake kuma tunanin zai iya zuwa da matsala.
Tsoffin daraktocin hukumar zabe mai zaman kanta da kuma masu hasashe a Najeriya sun yi gargadin cewa jam’iyyun siyasa na iya fuskantar rikici kan zaben fitar da gwanin da suka yi da kuma zabo abokan takarar a zaben shugaban kasa na 2023.
Tsofaffin jami’an alkalan zaben, wadanda suka zanta da jaridar Punch, sun gargadin cewa jam’iyyu da ‘yan takararsu na iya gamuwa da tasgaron rashin nasara a zaben shugaban kasa, idan wanda aka zaba a matsayin abokin takaran wucin gadi ya ki amincewa a sauya shi.
Wani batu da tsofaffin jami’an hukumar zabe ta INEC suka yi shi ne cewa jam’iyyu da ‘yan takararsu na iya rasa tikitin takara idan abokin takarar da bai cancanci zama mataimakin shugaban kasa ba ya ki janyewa daga takarar.
Yadda labarin ya faro Gabanin wa’adin da INEC ta sanya, da misalin karfe 6:00 na yamma a ranar Juma’a jam’iyyun siyasa da dama sun mika sunayen ‘yan takarar shugaban kasa na rikon kwarya.
Daga cikin su akwai dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, wanda ya zabi Kabiru Masari, a matsayin abokin gami.
Jam’iyyar Labour ta mika sunan Darakta-Janar na kungiyar yakin neman zaben Peter Obi, Dr Doyin Okupe, a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na wucin gadi na jam’iyyar.
Dukkanin jam’iyyun siyasa na da kwanaki 30 na janye sunayen wadannan ’yan takarar na wucin gadi tare da musanya su da wasu dalilai.
Sai dai tsofaffin manyan jami’an hukumar ta INEC da manyan lauyoyi sun bayyana ra’ayinsu game da tsarin.
Gargadi daga masana siyasa da makomar ta Wani tsohon Daraktan wayar da kan kan masu kada kuri’a a INEC, Nick Dazang, ya bayyana cewa ‘yan takarar na kokarin wucewa ta kofar da dokar zabe ta tanada ne kawai inda ta ce za a iya musanya abokin takara.
A cewarsa, ‘yan takarar shugaban kasa suna duba abokan takarar da za su ba da daidaito na kabilanci da addini ga tikitin su ne, suna kuma da kimar zabe da kuma iya kawo kuri’u a zabe.
Dazang ya kuma yi tsokaci kan abin da zai faru da tikitin idan abokin takarar bai cancanci zama mataimakin shugaban kasa ba.
Ya bayar da misali da yadda aka kai ruwa rana a zaben gwamna da ya gabata a jihar Bayelsa.
A ranar 13 ga Fabrairu, 2020, Kotun Koli ta soke zaben dan takarar jam’iyyar APC, Mista David Lyon, da abokin takararsa, Biobarakuma Degi-Eremienyo, a jajibirin rantsar da su kan wasu kura-kurai a cikin takardun abokin takara.
A bangaren wani tsohon Daraktan wayar da kan masu kada kuri’a a INEC, Oluwole Osaze-Uzi, ya bayyana cewa dokar ba ta amince da batun maye gurbin ba, inda ya kara da cewa “doka ta amince da ‘yan takara ne kawai” wadanda dole ne su cancanci mukaman da suke nema.
Ya kuma bayyana cewa “idan dan takara – wanda kuke kira na wucin gadi – ya ki janyewa, ba za a iya yin komai akai ba.”
A cewar Osaze-Uzi, za a iya maye gurbin dan takarar mataimakin shugaban kasa ne kawai idan ya janye da kansa sannan jam’iyya ta sanar da INEC cikin lokacin da doka da hukumar suka kayyade.
Matsayar INEC Game da cece-kucen, kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Festus Okoye, ya magantu kan matsayar INEC.
Ya ce kowace jam’iyya za ta iya maye gurbin abokan takara ta hanyar rubuta wasika hukumar INEC, da kuma hada wa da takardar shaidar kotu ta yin hakan.