Kamar yadda hedkwatan tsaron ta sanar, tace jirgin ya sauka a filin sauka da tashin jiragen na Kaduna sannan ya tarwatse, abinda yayi sanadin mutuwar shugaban sojojin.
Duk da Janar Lucky Irabor ya bukaci a cigaba da bincike a kan lamarin, ya bukaci a basu goyon baya tare da fahimta yayin binciken Hedkwatar tsaro ta kasa ta bayyana dalilin da ya kawo tarwatsewar jirgin sama wanda yayi sanadiyyar mutuwar shugaban sojojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da wasu sojoji 10 a ranar Juma’a, 21 ga watan Mayun 2021. Kamar yadda Onyema Nwachukwu, mai magana da yawun hedkwatar tsaro ya sanar, duk da ana cigaba da binciken abinda ya kawo hatsarin ya auku ne bayan jirgin ya sauka a filin sauka da tashin jiragen saman na Kaduna.
Duk da da dai, Nwacukwu ta shafin hedkwatar tsaron na Twitter, ya bayyana cewa Janar Lucky Irabor, shugaban ma’aikatan tsaro ya bada umarnin binciken lamarin da ya kawo mummunan hatsarin.
Mai magana da yawun hedkwatar tsaron yace: “Mummunan lamarin ya faru ne bayan saukar jirgin a filin sauka da tashin jiragen sama na Kaduna saboda yanayin gari mara kyau. “Shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor ya bukaci bincike domin gano dalilin da ya kawo hatsarin.
“A yayin da muke fatan rahama ga zakakuran dakarun sojin da shugaban sojin kasan, AFN na bukatar goyon bayanku da kuma fahimta daga dukkan ‘yan Najeriya a kan wannan lamarin da ya faru.”
A wani labari na daban, Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram ya sheka lahira yayin wata arangama da mayakan kungiyar ta’addanci ta ISWAP kamar yadda rahotanni suka bayyana.
A yayin bayyana wani bayanin sirri, Daily Trust ta ruwaito yadda shugaban kungiyar miyagun ta Boko Haram ya rasa rayuwarsa bayan musayar wuta da mayakan ISWAP.
A wani rahoton yadda lamarin ya faru, HumAngle ta ruwaito cewa wasu kwamandojin ISWAP sun rasa rayukansu tare da Shekau, da abinda ya kawo mutuwar tasu.