Abin da ya sa ake tuhumar gwamnatocin baya kan ‘kuɗin Abacha’
Wata Babbar Kotun Tarayya ta bayar da umarnin cewa a bayyana yadda aka kashe kuɗaɗe da suka kai dala biliyan biyar da ake zargin tsohon shugaban Najeriya Janar Sani Abacha ya sace amma aka ƙwato su tare da mayar wa ƙasar.
Bayanai sun ce an mayar wa Najeriya kuɗin da ake kira da ‘satar Abacha’ a lokacin mulkin shugabannin ƙasar kamar Olusegun Obasanjo da Umar Musa Yar’adua da Goodluck Jonathan da kuma Muhammadu Buhari.
Kotun ta kuma umarci gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta bayyana takamaimai yawan kuɗin da tsohon shugaban mulkin soji Janar Sani Abacha ya sace wa ƙasar da kuma dukkan abin da aka gano tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokraɗiyya.
Abacha ya mulki Najeriya, ƙasa mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka daga 1993 zuwa 1998, lokacin da Allah ya yi masa cikawa.
Kungiyar Transparency International mai fafutukar yaƙi da rashawa ta ƙiyasta cewa Abacha ya wawure dukiyar al’ummar Najeriya da ta kai dala biliyan biyar, inda ta ce kuma babu wanda ya taɓa gurfanar da shi gaban kotu a kan batun.
Wata ƙungiya mai rajin yaƙi da hanci da rashawa a Najeriya SERAP ce ta shigar da ƙara gaban kotun inda buƙaci a tilasta wa gwamnati bayyana kuɗaɗen almundahanar Abacha.
A tsawon shekaru da suka gabata, Amurka da Switzerland da kuma Birtaniya na cikin ƙasashen da suka mayar wa Najeriya ɗaruruwan miliyoyin daloli da ke da alaƙa da Abacha.
Kotun dai ta bai wa gwamnati umarnin ta fito ta yi bayani dalla-dalla a kan yawan kuɗin da Abacha ya sace da kuma yarjejeniyoyin da gwamnatocin Najeriya na baya suka cimma da ƙasashen waje don mayar wa ƙasar irin wannan dukiya zuwa yanzu.
Kungiyar SERAP wadda ta gabatar da ƙara kan batun, ta rubuta wa shugaba Tinubu wasiƙa a ranar Lahadi, inda ta yi kira gare shi da ya bi umarnin kotun.
Wani mai magana da yawun shugaban Najeriyar, Dele Alake bai mayar da martani kan saƙonni da aka aika wa fadar shugaban ƙasa don jin martaninta ba, in ji kamfanin dillancin labarai na Reuters.
A baya, Najeriya ta ce za ta yi amfani da wasu daga cikin kuɗin satar Abacha ne wajen gina ababen more rayuwa da suka haɗa da titunan mota da na jirgin ƙasa da kuma gadoji.
Da yake yanke hukunci kan batun a makon jiya game da ƙarar da ƙungiyar SERAP ta shigar, Mai shari’a James Olawole Omotosho, ya kuma umarci gwamnati, ta fito ta yi bayani kan irin ayyuka da yi da kuɗin satar Abacha, da wuraren da aka yi ayyukan da kuma sunayen kamfanonin da suka yi su.
Har ila yau, kotun ta bai wa gwamnatin tarayya umarnin yi mata bayani dalla-dalla a kan rawar da Bankin Duniya da kuma wasu suka taka wajen gudanar da ayyuka da kuɗin satar Abacha a ƙarƙashin tsoffin shugabannin Najeriya da suka haɗa da Obasanjo da Yar’Adua da Jonathan da kuma Buhari.
“Hanzarin da ministar kuɗi ta bayar na cewa ma’aikatar ta duba kuma ba ta ga wata takarda game da yadda aka kashe kuɗaɗen satar Abacha ba, da kuma ayyukan da aka yi da su, abu ne da ba za a lamunta ba. Saboda hakan ba shi da muhalli a sashe na bakwai na dokar ƴancin samun bayanai,” in ji Mai shari’an.
Omotosho ya ce gwamnati ta kasa bayyana wuraren da ta ce ta gina ababen more rayuwa da kuma sunayen kamfanonin da suka yi aikin ko suke ci gaba da ayyukan.