Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Nasarawa ta bayar da umarnin janye takardar shaidar cin zabe da aka baiwa gwamna Abdullahi Sule na jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18, ga watan Maris, 2023.
Kotun ta kuma bayar da umarnin ba dan takarar jam’iyyar PDP, David Umbugadu, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan.
Kotun mai alkalai uku ta yanke hukuncin ne ranar litinin, wanda ya tabbatar da Umbugadu a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.
A wani labarin na daban a safiyar ranar Litinin ne aka gurfanar da tsohuwar ministar albarkatun man fetur ta Nijeriya, Diezani Alison-Madueke, a gaban wata kotun majistare ta Westminster da ke birnin Landan da laifin karbar cin hanci bayan wani bincike da hukumar yaki da laifuka ta kasar Birtaniya NCA ta gudanar.
Diezani Alison-Madueke, mai shekaru 63, wadda kuma ta zama shugabar kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC, ta kasance jigo a gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2015.
A cewar NCA, Diezani ta karbi cin hanci a lokacin da take rike da mukamin ministar albarkatun man fetur a maimakon ta ba da kwangilolin man fetur da iskar gas na fam miliyan.
Ana zarginta da cin tsabar kuɗi har £100,000, motoci da jirage masu saukar ungulu masu zaman kansu da tara kayan alatu ga iyalint da kuma tara kadarori a London da daman gaske.
Har ila yau tuhume-tuhumen nata sun yi cikakken bayanin game da kayan da ake zarginta sama da fadi da su.
Aliso-Madueke, wacce a halin yanzu ke zaune a St John’s Wood, London, ta bayyana a Kotun Majistare ta Westminster a ranar Litinin, 2 ga Oktoba, 2023.
A ranar 22 ga watan Agusta ne LEADERSHIP ta gabatar da rahoton shugaban sashin yaki da cin hanci da rashawa na NCA (ICU), Andy Kelly, yana mai cewa: “Muna zargin Diezani Alison-Madueke ta yi amfani da karfinta a Nijeriya kuma ta karbi tukuicin kudi ta bayar da kwangiloli na miliyoyin ta hanyar da bata dace ba.
Source: LEADERSHIPHAUSA