Lauyan hukumar NDLEA ya kira Emeka Ezenwanne ya bada shaida a shari’ar Abbah kyari da ake yi a kotun tarayya.
Yanzu haka Emeka Ezenwanne yana garkame a gidan gyaran hali tun da aka kama shi da kwayoyi.
Mai laifin ya fadawa kotu yadda ya biya cin hanci a filin jirgi domin ya sulale da kwayoyi daga kasar waje.
Wani da aka kama da laifin safarar hodar iblis, Emeka Ezenwanne ya bada shaida a kotun tarayya na garin Abuja a shari’ar NDLEA da Abbah Kyari.
Premium Times tace Ezenwanne ne shaida na biyar da hukumar NDLEA ta gabatar, ya kuma yi bayanin yadda ya bada cin hanci wajen shigo da kwayoyi.
Kamar yadda Ezenwanne ya fadawa kotu da bakinsa, ya ba jami’an tsaron da ke aiki a filin jirgin Akanu Ibiam N10, 000, domin ya wuce dauke da hodar iblis.
Wannan mutum wanda yanzu yana daure a gidan yari da ke garin Suleja, yace an dauko hodar iblis din ne daga kasar Brazil, aka biyo da shi ta Habasha.
Mai bada shaidar ya fadawa Lauyan NDLEA, Joseph Sunday cewa ya je birnin Addis Ababa a tsakiyar Junairu domin ya karbo kwayoyi daga kasar Brazil.
“A ranar 16 ga watan Junairu da kimanin karfe 8:30 a agogon kasar Habasha, jirgin da ya zo daga Brazil ya sauka. Jim kadan bayan nan aka kira ni a waya.
Mutumin farko da ya kira ni a wayar salula, ana kiransa ‘Alhaji’.” – Emeka Ezenwanne.
“A ranar 19 ga watan Junairu da kimanin karfe 8:00 na safiya, muka hau jirgin da zai sauka filin sauka da tashin jiragen sama da ke garin Enugu.
Da muka isa filin jirgi, na fito na zauna a mota, ina jiran wanda muke tare da shi (Umeibe), ya fito.
Daga nan aka fara samun matsala, ‘yan sanda a cikin fararen kaya da muka gane cewa dakarun IRT ne, suka tare kayan da Umeibe ya dauko.
A filin jirgin saman Enugu, an bukaci In biya kudi ga mutanen da za su duba jaka ta.
Saboda haka sai na biya su N10, 000, suka kyale ni na wuce. – Emeka Ezenwanne IRT sun ankarar da NDLEA.
Vanguard ta rahoto Ezenwanne yana cewa daga baya ‘yan sandan suka fito da rigunansu, sai ya fahimci ‘yan IRT ne, a karshe suka cinna shi ga NDLEA.
Da aka zo gaban jami’an NDLEA, Ezenwanne yace adadin kwayoyin da suka shigo da su ya ragu, amma yace duk abin da aka yi, bai hau da DCP Abba Kyari ba.
Mai binciken Kyari ya mutu Kwanaki kun ji labari Joseph Egbunike, wanda shi ne Mataimakin Sufeta-Janar mai kula da sashen FCID na rundunar ‘yan sandan Najeriya ya kwanta dama.
Marigayi DIG Egbunike ne jami’in da IGP ya ba alhakin gudanar da bincike a kan DCP Abbah Kyari.
A halin yanzu an dakatar da Kyari, ana yin bincike a kansa.
Source:legithausang