Sashen Shari’a na Amurka ya sanar da dawowa Najeriya $20.6 miliyan a ranar Alhamis daga cikin kudin da Abacha da mukarrabansa suka wawure.
Tun a watan Augustan wannan shekarar aka saka hannu kan yarjejeniyar dawo da kudaden tsakanin gwamnatin Najeriya da ta Amurka.
Kamar yadda sashen ya bayyana, an dawo da kudin domin a kammala aikin gadar Niger ta biyu, titin Legas zuwa Ibadan da layin dogo na Abuja zuwa Kano don amfanin ‘yan kasa.
Sashin shari’a na Amurka yace an mayarwa Gwamnatin tarayya sama da $20.6 miliyan kamar yadda yarjejeniyar ranar 23 ga watan Augusta da aka yi tsakanin gwamnatin Najeriya da ta Amurka wurin maidawa Najeriya kudin da marigayi Janar Sani Abacha da mukarrabansa suka sata, jaridar Punch ta rahoto. Labari Mai Dadi: Amurka Ta Sake Dawowa da FG $20m na Kudin da Abacha ya Wawura.
Kamar yadda takardar da DoJ suka wallafa a shafin yanar gizonsu ya bayyana, dawo da wannan kudin yasa jimillar kudin da aka dawowa da Najeriya daga Amurka ya kai $332.4 miliyan.
A shekarar 2020, sashen ya dawo da $311.7 miliyan na kadarorin da aka kwace wadanda aka gano a Bailiwick ta Jersey.
A shekarar da ta gabata, Ingila ta yanke hukuncin sake dawowa da $20.6 miliyan zuwa Najeriya kan Amurka.
A 2014, an yanke hukuncin a yankin Columbia inda aka yi umarnin kwace $500 miliyan a wasu asusu dake fadin duniya sakamakon korafin da aka shigar na satar kudi da suka zarce $524 miliyan masu alaka da Abacha.
Kadarorin da aka kwace suna daga cikin kudaden rashawa wadanda aka adana su kamar na halas kuma bayan mulkin Abacha aka gano su.
Ayyukan da za a yi da kudin Takardar tace: “A karkashin yarjejeniyar da aka sa hannu a watan Augusta, Amurka ta yarda zata dawo da kashi 100 na kadarorin da aka kwace zuwa Najeriya domin taimakawa manyan ayyuka 3 a kasar da shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari da ‘yan majalisa suka amince da shi.
Gwamnatin Buhari “$20,637,622.27 ya nuna raguwa kadan daga $23 miliyan da aka sanar a watan Augusta saboda hawa da saukan canji tsakanin pan na Birtaniya da dalar Amurka.
“Kudin da aka dawo dasu a wannan yarjejeniyar za a yi amfani dasu wurin kammala gadar Niger ta biyu, babbar hanyar Legas zuwa Ibadan da babban titin Abuja zuwa Kano, lamarin da zai amfani kowanne ‘dan kasa a yankunan uku.”
Sashen ya yabawa taimakon da gwamnati Ingila, Najeriya, Jersey da Faransa suka hada wurin binciken.
Ya kara da cewa, lamarin ya zo gaban gwamnatin ne karkashin Kungiyar Samo kadarorin Sata wanda jajirtattun masu gurfanarwa a sashen yaki da wanke kudin haram da samo kadarori tare da hadin guiwar FBI suka gabatar.
An yi yarjejeniya Tsakanin FG da Gwamnatin Amurka A watan Augustan wannan shekarar Antoni Janar Abubakar Malami da gwamnatin Amurka sun sa hannu kan yarjejeniyar dawo da sama da $20m daga Amurka cikin kudin da Abacha ya sata. An yi wannan yarjejeniya ne a ma’aikatar shari’a dake Abuja.
Source:Legithausa