A Yau Ce Jam’iyyar APC Mai Mulki A Najeriya Take Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa.
Jam`iyyar APC mai mulki a Najeriya na gudanar da babban taronta na kasa, inda wakilai daga sassan kasar za su zabi sabbin shugabannin da za su gudanar da harkokin jam`iyyar nan da shekara huɗu masu zuwa.
Mutum tara ne suka nuna sha`awar tsayawa takarar shugabancin jam`iyyar, amma jiga-jiganta sun yanke shawarar bin hanyar maslaha a lokacin zaben.
Bakwai daga cikinsu, Mallam Saliu Mustapha da da Mallam Mohammed Etsu da da Sanata Mohammed Sani Musa da Sanata Tanko Al-Makura da Sanata George Akume da Senata Abdullahi Adamu duka daga shiyyar arewa ta tsakiyar Najeriya ne.
READ MORE : Rasha Ta Mayar Da Martani Kan Kalaman Biden Dangane Da Putin.
Sai na takwas, wato tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari daga shiyyar arewa maso yamma. Sannan akwai Sanata Ali Modu Sharif, wanda `yan kwanaki gabannin taron ya ce ya janye saboda ya hangi cewa akwai wani shiri da ake yi don daidaitawa a bar kujerar ga wani dan takara, kuma a cewarsa Shugaba Buhari na goyon bayan shirin maslaha ko daidaitawar.
Abdollahian; Bangarorin Vienna sun Kusa Cimma Yarjejeniya Kan Shirin Iran.