A Kalla Mutane 21 Ne Su Ka Rasa Rayukansu Sanadiyyar Wani Harin Taáddanci A Nijar .
A ranar Larabar da ta gabata ne dai aka kai harin taáddancin ayankin Telibaeri da ke kan iyakar kasar Nijar da Burkina Faso.
Majiyar a yankin da lamarin ya faru, ta shaidawa kamfanin dillancin labarun Faransa a jiya Alhamis cewa; Masu dauke da makamai ne su ka kai harin akan wasu motocin safa da ta daukar kaya, ya kuma yi sanadiyyar mutuwar mutane 19 da su ka hada da matafiya da ’yan sanda biyu.
Wata majiyar ta daban ta kuma shaidawa kamfanin dillancin labarun Faransan cewa; Wuta ta kama a cikin motar da mallakin wani kamfani ne na Najeriya.
READ MORE : Shugaban Kasar China Ya Bukaci A kawo Karshen Yakin Ukrain Da Gaggawa.
Matafiyan da suke cikin motar mai dauke da kayan marmari sun kone kurmus, yayin da mazauna cikin safa din su ka sami raunuka masu tsanani , kuma tuni an dauke su zuwa birnin Yamai domin samun magani.
An sami wasu mata 4 da kuma wasu maza 3 da su ka tsira daga harin.
‘Yan taádda masu jabun jihadi, sun addabi kasar Nijar da kasashen da suke makwabtaka da ita, da suka hada Burkina Faso, Mali da Najeriya.