DCP Abba Kyari ya nesanta kansa da wasu kadarori guda 14 da ake zargin gwamnatin tarayya ta bankado a matsayin mallakin sa.
Gwamnatin Tarayya dai tana zargin Kyari yana da wasu gidaje, shaguna da kadarori da ba a san da su ba Dakataccen shugaban na IRT ya ce naira miliyan 2.8 da wani N200,000 ne kacal da shi a cikin asusunsa na banki.
Dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, DCP Abba Kyari, ya karyata batun mallakar kadarori 14 da ake zargin gwamnatin tarayya ta bankado.
Kyari ya ce sabanin rahoton cewa an gano makudan kudade a asusun bankinsa, naira miliyan 2.8 ne kacal a asusunsa na UBA da kuma wani N200,000 a asusunsa na Sterling, jaridar Leadership ta rahoto.
Abba Kyari Ya Nesanta Kansa Da Kadarori 14 Da Aka Bankado.
A cewar wata sanarwa daga lauyansa, Barista Hamza Dan Tani, duk zarge-zargen da NDLEA ke yi dangane da kudade da kadarori mallakar Abba Kyari karya ne.
Dan Tani ya kuma bayyana cewa hukumar na batar da jama’a ne kawai don su yarda cewa dukiyoyin na Abba Kyari ne.
Ya kuma bayyana cewa yan kasuwar da suka mallaki wadannan kadarorin sannan suka bayar da takardunsu sun rigada sun shigar da hukumar NDLEA kara a babbar kotun tarayya na Maiduguri, Vanguard ta rahoto.
Wani bangare na jawabin ya ce: “An janyo hankalinmu zuwa ga wata wallafar karya a wasu sashin kafofin watsa labarai a ranar Litinin, 5 ga wata inda a jaridun aka ce gwamnatin tarayya ta bankado wasu kadarori 14 da suka hada da shaguna, gidaje, wurin wasan folo, filaye da gonaki mallakin tsohon kwamandan IRT, Abba Kyari, wanda ya kasance mataimakin kwamishinan yan sanda. “Muna son sanar da al’umma gaskiyar magana kai tsaye.
Shari’ar da NDLEA ke yi a kotu kan Abba Kyari da wasu hudu bata yi masu dadi ba.
Suna tsammanin shari’ar kotun zai tafi daidai tare da nasara a bangarensu kamar yadda shari’ar kafar labarai da suka dauki nauyi ya yadu a tsakanin Fabrairu da Afrilun 2022.
Sun gaza fahimtar cewa sabanin shari’ar midiya kotu na bukatar ainahin hujjoji na hakika wanda NDLEA bata da su a wannan shari’ar.”
Source: LEGITHAUSA