Hukumar DSS ta ƙasa ya saki, Ukamaka Ejezie, wacce aka fi sani da Mama Biafara, mahaifiyar Nnamdi Kanu daga tsare.
Shugabar tawagar lauyoyin Kanu, Ifeanyi Ejiofor, shi ne ya tabbatar da haka, ya ce zasu yi duk me yuwuwa su fitar da kowa.
Jami’an tsaro sun yi ram da matar ne a zaman Kotu da Kanu ya halarta na baya-bayan nan a watan Mayu.
Bayan shafe makonni a magarƙama, fitacciyar mai goyon bayan haramtacciyar ƙungiyar ƴan aware IPOB, Ukamaka Ejezie, wacce aka fi sani da Mama Biafara, ta samu yanci daga hannun jami’an tsaro.
Punch ta ruwaito cewa Mama Biyafara ta ɗauki shugaban IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, tamkar ɗan da ta haifa kuma an sako ta ne ranar Lahadi.
Shugaban tawagar lauyoyin da ke kare Kanu, Ifeanyi Ejiofor, shi ne ya tabbatar da sako matar a wata sanarwa da jaridar Punch ta ci karo da ita.
Ya ce, “Ina farin cikin sanar da ku cewa Misis Ukamaka Ejezie (Mama Biafra) ta samu yanci, yanzu ta fito daga magarƙamar hukumar DSS.
Godiya ga Chukwuokike Abiama, bisa wannan nasara.”
“Ba zamu huta ba duk wanda yake zaman Fursun kan wannan lamarin, har da wanda muke kare wa, Onyendu Mazi Nnamdi, ba da jima wa ba zasu shaƙi iskar ƴanci.”
“Mu a ɓangaren mu na shari’a, zamu yi duk me yuwuwa a kan doka ba don ganin mafarkin mu ya zama gaskiya, ba zamu huta ba kan alƙawarin mu, ina baku tabbacin haka, gaba dai gaba dai ba zancen koma wa baya.”
Yaushe aka kama Mama Biafara?
Mama Biafara, mai shekaru tsakanin 70-80, ta shiga hannun jami’an tsaro ne yayin zaman Kotun da Kanu ya halarta na ƙarshe ranar 18 ga watan Mayu, a Abuja.
Matar ta kasance tamkar mahaifiyar Nnamdi Kanu tun bayan rasuwar iyayensa a shekarar 2020.
A wani labarin kuma Rundunar Yan Sanda Ta Saki Sabbin Bayanai Kan Mutanen Da Suka Kashe Deborah, Ɗalibar Da Ta Taɓa Annabi SAW Rundunar yan sandan jihar Sakkwato ta fitar da sabon bayani kan Kes ɗin kisan Deborah Samuel, ɗalibar da ta yi batanci ga Annabi SAW.
Mai magana da yawun yan sanda, Sanusi Abubakar, ya ce sun baza komar su ta ko ina domin kama asalin makasan Deborah.
Source: LEGITHAUSA