Rundunar ‘yan sandan Jihar Delta da ke kudancin Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutum uku sakamakon rushewar da wani coci mai bene ya yi a birnin Asaba na jihar Delta.
Mai magana da yawaun rundnar ‘yan sandan jihar DSP Bright Edafe ne ya tabbatar wa da sashen BBC Pidgin labarin rushewar cocin na Pentecostal wanda fitacce ne a garin.
Ya ce “a daren jiya da abin ya faru, an ceto mutum 18 daga cikin ginin sannan mutum uku sun ji mummunan raunuka, zuwa safiyar yau kuma mutum uku sun mutu.
Sai dai DSP Edafe ya ƙaryata labaran da suka ce mutum 10 ne suka mutu. Wasu ganau na cewa har yanzu ana can ana aikin ceto.
Jami’in ƴan sandan ya ce mutanen da ke cikin cocin suna ibada a lokacin da abin ya faru a saman benen suke, don haka ginin bai faɗa a kan wasu ba a ƙsan.
Lamarin ya faru ne a jiya Talata da yamma lokaciin da masu ibada a cocin suke tsaka da addu’o’i na musamman bayan kammala wania zumi na kwana 21 dsa suka yi.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta Delta ta ce ƴan kwana-kwana da ƴan sanda na wajen don ci gaba da gano ko akwai waɗanda suka maƙale a cikin ɓaraguzan ginin don ceto su.