Gwamnatin jihar Kano ta ce, za a kammala aikin Dam ɗin Ƴansabo da ke karamar hukumar Tofa a farkon shekarar 2022.
Kwamishinan Muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya ba da wannan tabbaci lokacin da ya kai ziyarar duba yadda aikin ke gudana.
Ya ce, idan aka kammala aikin, al’ummar Ƴansabo, Tofa da makwabtan su za su ci gajiyar aikin sosai, musamman ta fannin noman rani da sauran ayyukan su na bunƙasa tattalin arziƙi.
Dakta Kabiru Getso ya bayyana jin daɗinsa bisa yadda aikin ya kai wani mataki a yanzu, har ma ya ce, tuni aka biya diyya ga manoman da aikin ya biyo ta gonakin su kuɗaɗe da ya kai Naira miliyan 70.
Bankin Duniya ne ya saukar nauyin aikin samar da Dam ɗin a yankin na Ƴansabo ƙarƙashin hukumar (NEWMAP) kama yadda sanarwar da mai magana da yawun ma’aikatar Sunusi Abdullahi Ƙofa Naisa ya fitar.