A halin yanzu dai manyan jam’iyyun siyasar Nijeriya guda biyu wato APC da PDP suna kokarin shawo hanyoyin da za su bi wajen warware matsalolin rikicin cikin gida kafin fara Shirin babban zaben 2023 gadan-gadan.
Jam’iyyar APC ta kasance karkashin shugabancin kwamitin riko wanda Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni yake jagoranta bayan gushewar tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, yayin da jam’iyyar PDP a halin yanzu ta kasance karkashin shugabancin mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa, Elder Yemi Akinwonmi bayan da wasu kotuna guda biyu da suke zaune a jihohin Ribas da Kuros Ribas suka sauke shugaban jam’iyyar na kasa, Prince Uche Secondus.
Lokacin da aka nada Mala Buni a matsayin shugaban riko na jam’iyyar APC, an ba shi wata shiga ya gudanar da babban taron jam’iyya wanda zai bayar da damar zaben shugabannin jam’iyya na kasa bayan rushe shugabancin Adams Oshiomhole da kwamitin amintattu na jam’iyyar APC suka yi a ranar 25 ga watan Yunin shekarar 2020. Amma a ranar 8 ga watan Disambar shekarar 2020, an kara tsawaita wa’adin shugabancin kwamitin riko domin samun damar gudanar da rijistar mambobin jam’iyyar.
An ci gaba da kara wa’adin shugabancin kwamitin riko a cikin jam’iyyar APC, wanda masu ruwa a tsaki a cikin jam’iyyar suka ga ya kamata jam’iyyar ta samu zababben shugaba wanda zai ci gaba da jan ragamar shugabancin jam’iyyar.
Saboda haka, wata babbar kotu da ke zama a Asaba cikin Jihar Delta ta hana Gwamna Buni da wasu mambobi su dunga daukar kansu a matsayin shugabannin riko na jam’iyyar APC har sai ta yanke hukunci a kan karar da aka shigar a gaban kotun. Amma an yi watsi da wannan umurnin kotu.
Wani dan jam’iyyar daga Jihar Delta, mai suna Mista Christian Abeh ya shigar da kara a babbar kotun da ke zama a Asaba wajen hana Gwamna Buni ya gabatar da kansa a matsayin shugaban riko na jam’iyyar APC.
Haka kuma, wasu masu ruwa da tsaki a cikin jam’iyyar APC sun bayyana wa manema labarai cewa akwai bukatar jam’iyyar ta samu sahihin shugaba da zai iya warkar da jam’iyyar game da rashin lafiyar da take fuskanta da kuma gudanar da shugabanci nagari a kowani lokaci. Sun kara bayyana cewa bayan wadannan siffofi, ya kamata shugaban ya kasance yana da ilimin gudanar da harkokin jam’iyya wanda zai iya dinke barakar da ke cikin jam’iyyar ta hanyar sadaukar da kai ga jam’iyyar.
Mafi yawancin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sun nuna sha’awarsu na tsayawa takarar neman shugabanin jam’iyyar. Sai dai wasu ba su bayyana hakan a hukumance ba, amma wasu daga cikinsu sun bayyana sha’awarsu a fili na neman shugabancin jam’iyyar wadanda suka hada da tsohon gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Madu Sheriffi da tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulazeez Abubakar Yari da Abdullahi Adamu da Tanko Al-Makura da Danjuma Goje da kuma George Akume.
Wani jigo a jam’iyyar APC mai suna Hon. Bernard Mikko daga Jihar Kuros Ribas ya bayyana cewa a cikin wadanda suke neman takarar shugabancin jam’iyyar APC a nasa ra’ayi yana ga tsohon gwamnan Jihar Borno, Ali Modu Sherriff ya fi sauran cancanta, domin yana ganin zai iya hada kai ‘ya’yan jam’iyyar. Ya kara da cewa ya samu nasarar rike mukamin gwamnan Jihar Borno har sau biyu, sannan kuma ya kasance dan majalisar dattawa, wanda hakan zai iya ba shi damar zama kyakkyawan shugaban jam’iyyar saboda yana da kwarewa da kuma siffofin shugabanci.
Shi ma da yake tattaunawa da manema labarai a ranar Alhamis da ta gabata a garin Abuja, tsohon mashawarcin gwamnan Borno, Kashim Shettima kan harkokin siyasa, Mustapha Gambo ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar APC da sauran masu ruwa da tsaki su goyi bayan Sheriff a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa. Da yake bayanin dalilan da ya kamata shugabannin jam’iyyar su goyi bayan Sheriff, Gambo ya bayyana cewa Sheriff ya san duk lamuran da suka shafi jam’iyyar APC, sanna ya kuma ce jam’iyyar za ta samu gagarumar nasara a zaben shekarar 2023.
Masu sharyi a kan al’amuran siyasa sun bayyanaa cewa jam’iyyar APC tana bukatar samun tsayayyen shugaba wanda zai iya jagorantar jam’iyyar musamman ma a yanzu da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake kokarin kammala wa’adin mulkinsa.
A bangare daya kuma, babbar jam’iyyar adawa ta PDP tana fama da rikicin shugabanci, inda a makwannin da suka gabata jam’iyyar ta kara tsunduma cikin rikicin shugabanci. Rikicin ya ci gaba da ruruwa wanda har ta kai da yin awon gaban da shugabancin Prince Uche Secondus a matsayinsa na shugaban jam’iyyar a baya.
Sakamakon zazzafar muhawara da ta sarke jam’iyyar, kwamitin zantarwa na jam’iyyar PDP ya saka ranar 30 zuwa 31 ga watan Oktoba domin gudanar da babban taro wanda zai bayar da dama a zabi shugabannin jam’iyya, yayin da a yanzu aka zabi mambobin kwamitin amintattu a matsayin wadanda za su ci gaba da jan ragamar shugabancin jam’iyyar.
A halin yanzu dai, mafi yawancin ‘ya’yan jam’iyyar sun nuna sha’awarsu na tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar. Yayin da wasu daga ciki suka musanta, sannan wasu suka kasa fitowa su bayyana a hukumance.
‘Ya’yan jam’iyyar PDP kamar irin su Cif Olabode George, Cif Raymond Dokpesi da kuma dan takarar gwamnan a Jihar Ondo karkashin jam’iyyar PDP, Mista Eyitayo Jegede da dai sauran su, dukkansu sun nisanta kawunansu na ikirarin da ake cewa za su nemi takarar kujerar shugabancin jam’iyyar.
Amma har yanzu shi Olagunsoye Oyinlola yana musanta cewa ya nuna sha’awa duk da sau da dama ana fadin sunansa a matsayin na gaba-gaba wajen neman shugabancin kujerar jam’iyyar PDP.
Da yake zantawa da gidan talabijin na Channels TB a cikin shirin siyasa na ranar Lahadi kan mutumin da ya dace ya shugabanci jam’iyyar PDP, Sanata Walid Jibrin ya bayyana cewa a yanzu haka jam’iyyar PDP tana bukatar shugaba jajirtacce wanda ba zai karkata gefe daya ba, zai kasance mutum na kowa da kowa.
Ya ce, “A wannan lokaci da muke ciki a yanzu haka, muna bukatar yin magana da murya daya wajen zaban shugaban jam’iyyarmu na kasa da zai jagoranci wannan jam’iyyar ta PDP. Ya kamata mu sami mutumin da zai iya jagorantar wannan jam’iyyar tamu. Shugaban ya kasance gogaggen dan siyasa a mataki na tarayya da kuma ta jiha tare da kyakkyawan siffofin shugabanci. Mutumin da zai yi tafiya da kowa daga cikin mu, ba wanda zai nuna bangaranci ba.”
Da alama dai rikicin shugabancin da ya sarke manyan jam’iyyun siyasar Nijeriya ya zama karfen kafa wanda zai iya hana jam’iyyun fitar da kwararran dan takara da zai dace da Nijeriya. Koma dai mene ne, ‘yan Nijeriya suna dako su ga irin shugaban jam’iyyar da PDP da APC za su fitar domin samun damar fitar da dan takarar da ya dace.
2023 2023 2023 2023 2023 2023 2023 2023