Jam’iyyar Kwankwaso watau NNPP mai kayan marmari ta samu gagarumin karin goyon baya yayin da ake fuskantar zaben 2023 a jihar Gombe.
Mambobin majalisar dokokin jihar guda biyu sun sauya sheka daga APC mai mulki zuwa inuwar NNPP.
Wannan ci gaban ya ƙara karfi ga ɗan takarar gwamnan Gombe na NNPP kuma jam’iyyar ta zama babbar mai adawa.
Ɗan takarar gwamna a inuwar jam’iyyar NNPP a zaben 2023 a Jihar Gombe, Khamisu Mailantarki ya samu gagarumin goyon baya yayin da ‘yan majalisu biyu a jihar suka fice daga APC.
Jaridar Tribune Online ta rahoto cewa ‘yan majalisun sun haɗa da, Honorabul Hamza Adamu mai wakiltar Balanga ta kudu da Bappa Usman Jurara, mai wakiltar Funkaye ta kudu a majalisar dokokin Gombe.
Rahoto ya nuna cewa mambobin majalisar guda biyu sun sauya sheƙa daga APC zuwa NNPP ne bayan ganawa da ɗan takarar gwamna, Khamisu Ahmed Mailantarki.
Wannan ci gaban na zuwa ne awanni kalilan gabanin kaddamar da fara yakin neman zaɓen jam’iyyar NNPP a 2023, wanda aka tsara gudanarwa ranar Asabar.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa bayan wannan sauya sheka, NNPP ta zama babbar jam’iyyar adawa a jihar Gombe, tana da ‘yan majalisu a majalisar dokoki.
Meyasa suka ɗauki matakin komawa NNPP?
Da suke hira da wakilin jaridar jim kaɗan bayan sauya sheka zuwa NNPP, mambobin majalisar biyu sun ce sun yanke haɗa hannu da Mailantarki ne domin kishin jihar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Sun bayyana cewa manyan ‘yan takara biyu da ake kallon su ne na sahun gaba, na APC da PDP, ba su da nagartar shugabanci da ake buƙata wajen haɗa kai da kawo ci gaba a Gombe.
Idan baku manta ba a ‘yan kwanakin nan, da yawan mambobin APC da PDP, waɗanda suka fusata da wani rashin adalci a jam’iyyunsu na ci gaba da turuwar komawa NNPP.
A wani labarin kuma Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa ya nesanta kansa da wani bidiyo da ya nuna yadda aka yi wa wani mutumi tsirara Bidiyon wanda aka yaɗa a kafafen sada zumunta an yi zargin cewa wasu matasa ne suka yi wa Abdullahi Adamu tsirara a fadar mai martaba Sarkin Lafiya.
Da yake karyata raɗe-raɗin ta bakin hadiminsa, Malam Muhammed, yace zargin ƙanzon kurege ne, ko kaɗan mutumin bai yi kama da shi ba.