Ifeanyi Okowa ne wanda Alhaji Atiku Abubakar ya zaba a matsayin abokin takararsa a Jam’iyyar PDP a 2023.
Gwamna Nyesom Wike ne zai zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023 Babu mamaki Atiku yana ganin Dr. Okowa zai fi dacewa da shi a kan tsohon abokin hamayyar sa.
A wannan rahoto, Daily Trust ta kawo dalilan da ake zagin su ne suka jawo Atiku Abubakar ya dauki Dr Ifeanyi Okowa, a maimakon Nyesom Wike.
1. Yakin neman tikiti Atiku Abubakar da Nyesom Wike sun gwabza wajen neman tikitin PDP na zaben 2023, inda Gwamnan ya nemi ya kawowa Wazirin Adamawa babbar barazana.
Nyesom Wike ya yi ta sukar wadanda suka bar PDP a 2014 a wajen kamfe da yake yi, ko da Atiku bai taba tanka shi ba, hakan ya nuna ‘yar tsamar da ke a tsakaninsu.
Saboda Atiku Ya Zabi Okowa a Matsayin Mataimakinsa, Zai Koma Yi Wa Tinubu Kamfen.
2. Dabi’ar Wike Jaridar ta na zargin halayar Gwamnan na Ribas da irin dabi’arsa ta jawo Atiku Abubakar wanda ba mutum ba ne mai hayaniya, ya ki zaben shi a matsayin abokin takara.
Shi Wike mutum ne mai hayaniya da fadan duk abin da ya zo masa ba tare da jin wani tsoro ba.
A gefe guda kuwa, Ifeanyi Okowa ya na yanayi da ‘dan takaran na PDP.
3. Kokari a zaben fitar da gwani Legit.ng Hausa ta na zaton Sanata Okowa ya taka rawar gani wajen nasarar da Atiku Abubakar ya samu a zaben fitar da gwani, inda ya doke Nyesom Wike da wasunsa.
Sakayyar da Atiku zai yi wa Okowa shi ne ya dauke shi a matsayin mataimaki. Daukar Wike zai zama Okowa ya yi biyu babu a 2023 bayan ya yi fada da makwabacin na sa.
4. Atiku v Wike Tun can dai babu jituwa sosai tsakanin Atiku Abubakar da Gwamna Wike. Rahoton ya ce a zaben fitar da gwani na 2018, Wike ya goyi bayan Aminu Tambuwal a kan Atiku.
Nyesom Wike bai kallon Atiku a matsayin abokin tafiya, sai ma wanda ya baro APC zuwa jam’iyyar APC domin ya yi takara da shi bayan sun gama wahala da jam’iyya.
5. Kalaman Nyesom Wike Wasu maganganun Wike za su iya zama matsala a gare shi.
Da bakinsa ya taba nuna kiyayyarsa ga Atiku, kuma ya taba cewa bai sh’awar kujerar mataimakin shugaban kasa. Haka zalika za a iya amfani da wasu babatun Gwamnan na jihar Ribas a yankin Arewacin Najeriya domin a kawowa takarar Atiku da PDP barazana a zaben mai zuwa.