Tsohon mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar APC na kasa, Kwamared Timi Frank, ya yi kira ga hukumar zabe INEC, da ta gaggauta Dakatar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. a zaben 2023.
Frank a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Lahadi, ya kuma yi kira ga jam’iyyar APC da ta maye gurbin Tinubu a matsayin dan takararta na shugaban kasa idan har tana fatan kasancewa a zaben shugaban kasa a 2023.
Dan gwagwarmayar siyasar, haifaffen Bayelsa ne ya ce hakan ya zama dole biyo bayan zargin rashin kaddamar da takardun makarantar dan takarar APC kamar yadda yake kunshe a kundin INEC wanda ta buga kwanan nan.
Frank, wanda shi ne jakadan kungiyar United Liberation Movement for West Papua (ULMWP) a Gabashin Afirka da Gabas ta Tsakiya, ya ce batun takardar shedar Karatu ta Tinubu ko rashinta.
Wannan wani gwaji ne na Tabbatar da cewa Hukumar Zabe ta kasa mai zaman kanta INEC za ta sauke alhakin dake kanta na tabbatar da tantance dan takara ko za tayi bangaranci a babban zaben shekarar 2023 dake gabatowa?
Ya kara da cewa kin gabatar da takardun shaidarsa na karatu kamar yadda doka ta tanada ga wadanda ke neman mukaman siyasa a kasar nan, Tinubu kai tsaye, bai dace ya shiga takarar shugaban kasa ba. na 2023 ba.