National Democratic Institute % International Republican ta gabatar da bincikenta a kan zaben 2023.
Cibiyar ta nuna zai yi wahala a iya samun wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasa a kai tsaye Hakan zai bayu ne saboda kananan jam’iyyu irinsu LP da NNPP sun tsaida manyan ‘yan siyasa.
Zaben da za ayi a 2023 zai iya zuwa da abubuwan mamaki, cibiyar National Democratic Institute and International Republican ta bayyana haka.
Dazu ne Jaridar The Guardian ta rahoto cewa National Democratic Institute & International Republican Institute tayi wannan bayani a ranar Juma’a.
Cibiyar ta ce akwai yiwuwar zaben shugaban kasar 2023 ba zai kammalu a zagayen farko ba a dalilin tsayawa takarar Dr. Rabiu Kwankwaso da Peter Obi.
Binciken da cibiyar ta gudanar ya nuna zaben 2023 zai sha ban-bam da sauran zabuka da aka yi.
Shugabannin kungiyoyin NDI/IRI a karkashin jagorancin Frank LaRose suka bayyana haka yayin gabatarwa manema labarai binciken da suka yi.
Kamar yadda masanan suka bayyana a rahotonsu, takarar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ta kayatar da matasa, kuma za su iya kawo cikas a zabe.
Punch ta rahoto wannan bayani wanda ya nuna irin sarkakiyar da ke tattare da zabe mai zuwa. Sakamakon binciken da aka yi
“Idan kananan jam’iyyu suka samu isasshen goyon baya, watakila akwai yiwuwar zaben ya kai ga zagaye na biyu, a karon farko da dawowar farar hula.”
“Zabukan 2023 sauyi ne daga abin da aka saba a siyasar da aka gani a baya. Tun 2007 sai yanzu za a shiga zabe ba tare da mai mulki yana takara ba.”
“APC mai mulki ta tsaida tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu. PDP ta tsaida tsohon mataimakin shugaban kasa kuma ‘dan takaran 2019, Atiku Abubakar.
Tsohon gwamnan Anambra, ‘dan takaran LP da Rabiu Kwankwaso – Tsohon gwamnan Kano, ‘dan takaran NNPP ya burge matasa.”
Rahoton ya nuna wadannan kananan ‘yan takara za su iya hana a samu wanda ya yi nasara a zaben Sowore ya caccaki Atiku da Obi.
A makon nan aka ji labari Omoyele Sowore ya yi wa Atiku Abubakar martani da yake maganar yadda zai gyara harkar wutan lantarki idan ya karbi mulki.
Sowore yake cewa Atiku na da hannu wajen jawo tabarbarewar lantarki a gwamnatin Obasanjo, bayan nan kuma matashin ya caccaki Peter Obi.
Source:hausalegitng