Allah ya yi wa jarumin masana’antar shirya fina-finai Aminu Mai Khamis, wanda aka fi sani da Mai Mala na cikin shirin ‘Dadin Kowa’ mai dogon zango na gidan talabijin na Arewa24 rasuwa.
Wannan na cikin wani sako da daya daga cikin marubuta labarin Dadin Kowa, Nazir Adam Salih ya wallafa a shafinsa na Facebook.
“Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un. Aminu Mai Kamis (Kawu Mala) a shirin Dadin Kowa lokaci ya yi.
“Allah Ya jikan dan uwa, babban yaya kuma aboki mutumen kirki. Ban taba ganin fushinsa ba a shekaru sama da 30,” kamar yadda ya wallafa.
Jarumin ya rasuwa ne a Lahadi da daddare kuma an ruwaito cewar za a yi jana’izarsa da safiyar ranar Litinin a gidansa da ke unguwar Hotoron Arewa a titin Ring Road da ke Kano, kamar yadda wata majiya daga iyalinsa ta bayyana.
Cikakken bayani na tafe…