A wannan Asabar ake gudanar da bukukuwan cika shekaru 63 da kasancewar Nijar, kasa kuma Jamhuriyar. A kowace shekara hukumomin Nijar na zabar jihar da zata karbi bakuncin gudanar da bikin.
A wannan karon birnin Diffa ne ke karbar nauyin gudanar da bikin, mai taken Diffa N’glaa. Ana faretin soji kana kuma akan kaddamar da manyan ayyuka na gine gine da akayi a birnin dake karbar bakuncin bikin.
A jajibirin bikin kamar yadda a al’ada shugaban kasar kan yi jawabi ga al’umma. A cikin jawabin nasa ya tabo batun matsalar dake addabar kasar da sauren kasashen yankin.
Ya kuma jinjinawa jami’an tsaron kasar kan tsayin daka a yaki da gungun ‘yan ta’dda, dama sojojin da suka rasa rayukansu wajen kare kasar.
Read more : https://nigeria21.com/hau/siyasa/dakarun-jamhuriyar-nijar-11-ne-suka-mutu-a-harin-dagne/