Wani ɗalibi mai suna Babangida Ahmad, wanda ke karatu a Sashin Laburare da Kimiyyar Yaɗa Labarai na Jami’ar Bayero Kano, BUK, ya rasu.
A wata sanarwa da Mataimakin Rijistara, Fannin Hulɗa da Jama’a na Jami’ar, Lamara Garba ya fitar, ɗalibin, wanda ya ke matakin gyran jarrabawa ta shekarar ƙarshe, ya rasu ne a jiya Juma’a a ɗakin kwanan ɗalibai.
An ce marigayin wanda ya fito daga garin Misau da ke Jihar Bauchi, ya faɗi ne da sanyin safiyar Juma’a a ɗakin kwanan ɗalibai a lokacin da ya ke shirin zuwa masallaci domin yin sallar asuba, kamar yadda abokan zamansa su ka baiyana.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “A cewar ɗaya daga cikin abokan zamansa, marigayi Ahmad ya fita daga dakin da misalin karfe 4:30 na safe, inda nan take sai ya faɗi ba tare da wata alamar yana numfashi ba, tun kafin ma a garzaya da shi zuwa asibitin jami’ar da ke cikin harabar makarantar.”
“An ce ma tuni ya rasu tun kafin ma a ƙarasa da shi zuwa asibitin Jami’ar.”
Sanarwar ta ce kafin rasuwarsa, marigayin ya ziyarci asibitin koyarwa na Aminu Kano inda ya ke ganin likita kan wata cuta da ba a bayyana ba.
Kamar yadda bayanan asibiti suka nuna, an ga ya ziyarci Asibitin Koyarwa na Aminu Kano kusan sau bakwai a cikin shekara daya, inda ya kai ziyarar ta karshe a ranar 10 ga Janairu, 2022.
A halin da ake ciki dai Hukumar Jami’ar ta ɗauki gawar zuwa garinsu domin binne shi.
A madadin Shugaban Jami’ar, Sagir Abbas, yana mai yiwa ‘yan uwa da abokan arziki na marigayin ta’aziyya tare da addu’ar Allah ya jikansa da Jannatul Firdaus.
An bayyana Marigayi Babangida Ahmad a matsayin mutumin kirki, mai son barkwanci da kuma sada zumunci, wanda ke da kyakkyawar alaƙa da abokan karatunsa.