Ƴan takarar jam’iyyun adawa ba su san hanya ba balle su nuna wa wani – Tinubu.
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC a Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi alwashin magance matsalolin da ke damun kasar idan ya samu nasarar karbar mulki a babban zaben da ke tafe.
A yau ne dan takarar ya kaddamar da yakin neman zaben nasa a Jos, babban birnin jihar Filato, wanda Shugaba Buhari da sauran jiga-jigan jam’iyyar suka halarta.
Mista Bola Tinubu ya lissafa mafi yawan matsalolin da ke damun Najeriya, ciki har da ƙarancin abubuwan more rayuwa, da durƙushewar masana’antu, da rashin aikin yi a tsakanin matasa.
Kana ya yi alwashin magance su ta hanyar haɗa ƙwararru kuma gogaggu a cikin gwamnatinsa idan ya samu nasarar kafawa.
“Mu a jam’iyyar APC, wato Tinubu da Shetima da yardar Allah mun yi wa ƴan Najeriya alkawarin yin shugabanci nagari a karakashin wannan yunƙuri na farfadowa ko sabunta fatan alheri a zuƙatan al’umma, sakamakon goyon bayan da kuke ba mu. Za mu hada ayarin jarumai don ciyar da kasa gaba.”
Kazalika, dan takarar shugaban kasar ya caccaki abokan hamayyarsa… musamman ma na jam’iyyun adawa da ke gaba-gaba, wani lokaci har da kiran suna yana gugar-zana, yana cewa ba su san hanya ba, ballantana su yi wa wani jagora.
Shi ma abokin takararsa, wato tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shetima da ya hau dandamali, bai ragar wa abokan hamyayyar nasu ba, yana cewa idan ka ji mutum ya ce zai ba ka riga to ka dubi ta wuyansa.
Duk da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci wajen taron amma bai ce komai ba, face danƙawa ɗan takarar tutar jam’iyya da ya yi.
Sai dai daya daga cikin gwamnonin da suka yi jawabi, Gwamna Nasiru ElRufai na jihar Kaduna, ya mayar da raddi ga masu kushe dan takarar yana cewa shi ne zabin manya.
Da dama da suka yi jawabi sun nuna suna da kwarin gwiwa APC za ta kai labari a zabe mai zuwa.
Amma Shugaban jam’iyyar APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu ya shawarci ƴan jam’iyyar da ka da su shagala, su bari mulki ya ruɗe su, su yi wa jam’iyya aiki idan suna so su ga alheri.
“Kasancewa a kan karagar mulki ba ya sa a dauwama a kan mulki. Ba zai hana faduwa ba idan ba mu dage mun yi abin da ya kamata mu yi da zai ma samu karbuwa a zukatan masu kaɗa ƙuri’a ba.
“Wannan ne ya sa nake jaddada cewa mu kasance masu himma. Mu hada kai ta yadda za mu gudu tare mu tsira tare.”
An dai kammala taro ana ta annashuwa, amma wani suɓul-da-baka da dan takarar shugaban kasar ya yi ta janyo ce-ce-ku-ce, lokacin da zai yi fatan alheri ga jam’iyyar a karshen jawabinsa sai ya ɓuge da ambaton sunan jam’iyyar adawa!