Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Kano ta gaiyaci Muaz Magaji, wani ɗan adawar Gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
A Bara ne dai Ganduje ya sallami Magaji da ga muƙamin sa na Kwamishinan Aiyuka da Gine-gine sakamakon kalaman da ba su dace ba a kan rasuwar Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Ƙasa, Abba Kyari.
Tun da ya bar gwamnatin Ganduje, sai Magaji, wanda a ka fi sani da Ɗan-Sarauniya, ya ke yiwa gwamnan adawa kan irin salon mulkin sa da kuma zargin saka iyalin sa a cikin mulki.
Da ga bisani sai tsohon Kwamishinan ya koma ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau bayan da jam’iyar APC ta tsaye gida biyu a jihar.
Da ya ke tabbatar da gaiyatar ga Daily Nigerian Hausa, Magaji ya ce ƴan sandan sun kira shi ne a waya cewa ya je shalkwatar domin tambayoyi.
Ya ce gaiyatar na da nasaba da irin adawar sa ga gwamnatin Ganduje.
Sai dai kuma Kakakin Rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce sun gaiyace shi ne sakamakon ƙorafi da a ka shigar a kan sa.