Ƙarancin man dizal ya jefa Sri Lanka cikin matsalar wutar lantarki.
Gwamnatin Sri Lanka ta bayyana cewa ta yi ƙoƙarin biyan kusan dala miliyan 35 domin shigar da man dizal cikin ƙasar a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar ɗauke wuta.
Sri Lanka kuma na fama da matsala a asusun ajiyarta na waje wanda hakan ya kawo cikas ga biyan kuɗaɗen shiga da kayayyaki ƙasarta ciki har da abinci da man fetur.
Ƙasar na buƙatar kimanin tan dubu huɗu na man dizal a kullum domin tafiyar da injinan samar da lantarki na ƙasar kuma ƙarancin man ya jawo ɗaukewar wuta a sassan ƙasar.
Haka kuma shi ma man fetur ya yi ƙaranci a ƙasar wanda ya jawo layukan mai a ƙasar.