Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a tarayyar Najeriya ta dage aiwatar da shirinta na cire tallafin man fetur a kasar zuwa wani lokaci.
Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto ministan kudi Zainab Ahmed tana fadar haka bayan wata tattaunawa da tayi da shugaban majalisar dattawar kasar Ahmed Lawal.
Labarin ya kara da cewa, maimakon hakan gwamnati zata yiwa kasafin kudin wannan shekara koskorima don dagewar, sannan zata maida hankalin wajen ganin an kammala aikin gina matatan man fetur ta Dan Gode, da kuma wasu ayyukan gyare-gare a matatun man kasar kafin a sake dawo da batun.
A nashi bangaren shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawal ya bayyana cewa wannan lokacin bai dace a cire tallafin man fetur a kasar ba, don irin wahalhalun da mutane zasu fada ciki. Kafin haka dai gwamnatin tana son cire tallafin ne a cikin watan Yuli mai zuwa.