Fiye da gawakin mutane 50 ne aka gano a wasu garuruwa a karamar hukumar Anka da Bukkuyum na jihar Zamfara bayan wasu mummunan hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a ranar Talata da Laraban da suka gabata.
Jaridar Premium Times ta Najeriya ta nakalto wani wanda ya fito daga garin Waramu yana cewa sun gano gawakin mutane 58 ya zuwa lokacin bada wannan rahoton a jiya Jumma’a.
Labarin ya kara da cewa har yanzun tawagar wasu daga cikin wadanda suke da sauran shan ruwa suna bin dazuzzuka don gano wasu karin gawaki idan akwai.
Hamza Adamu wani mutumin yankin ya fadawa Premium times kan cewa Gambo Abare shugaban mayakan sa kai masu taimakawa jami’an tsaron kasa na daga cikin wadanda ‘yan bindigan suka kashe.
Har’ila yau wani wanda ake kira Murtala Waramu ya fadawa VOA Hausa kan cewa sun gano gawaki 58 sannan suna kan neman karin gawaki a jiya Jumma’a.
Banda haka ya ce banda kissan mutane ‘yan bindigan sun kona gidaje da shagunan mutane a garuruwa da dama a yankin.