Ƴan sanda sun gargadi masu ɗaukar doka a hannu kan waɗanda ake zargi da satar al’aura
Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Babban birnin tarayya ta gargaɗi mazauna yankin kan ɗaukar doka a hannu kan waɗanda ake zargi da aikata laifuka, domin gudun tayar da zauna tsaye.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta hannun jami’arta ta yaɗa labaru da hulɗa da jama’a, SP Josephine Adeh, ta ce ta yi gargaɗin ne bayan yunƙurin da wasu mutane suka yi na hukunta wani mutum da aka zarga da satar al’aura a yankin Karshi na babban birnin tarayyar.
Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata, inda wasu maza uku suka ce sun ji wani yanayi da ba su gane ba a al’aurarsu bayan haɗa jiki da mutumin.
Bayan hakan ne dandazon mutane suka far wa wanda ake zargin, sai dai jami’an ƴan sanda sun ceci shi sa’ar da suka isa wurin, jim kaɗan bayan bayan fara ɗaukar matakin.
Dalilin haka ne kwamishinan ƴan sanda na yankin birnin tarayyar, CP Haruna G. Garba ya buƙaci jama’a da su guji ɗaukar irin wannan mataki.
A cikin kwanakin nan an riƙa yaɗa labaru, waɗanda ba a tantance ba kan ɓullar mutane masu satar al’aura bayan haɗa jiki ko kuma shan hannu da al’umma.